Yoweri Museveni: Shin shugaban Uganda yana son yin mulki har abada?

Matakin da Shugaba Yoweri Museveni ya dauka na sake tsayawa takarar shugabancin Uganda a shekarar 2021 ya bijiro da tambayoyi da dama, cikin su har da cewa: shin so yake ya zama shugaban kasa na mutu-ka-raba?

Ranar Talata Shugaba Museveni, wanda ya kwashe shekara 36 yana mulkin kasar, ya ce zai tsaya takara a koro na shida.

A watan Mayu na shekarar 2016 Mr Museveni ya sha rantsuwar kama aiki a karo na biyar bayan zaɓukan da aka yi ta taƙaddama a kai.

Idan ya sake yin nasara a zaben, shugaban na Uganda mai shekara 75, zai yi mulki tsawo shekara 40 kenan.

"E, muna tabbatar da cewa ya karbi takardar tsayawa takara domin zama dan takararmu," a cewar Rogers Mulindwa, mai magana da yawun jam'iyya mai mulkin kasar National Resistance Movement (NRM), a hirarsa da kamfanin dillacin labarai na Reuters, yana mai karawa da cewa babu wanda ya fito ya bayyana sha'awar tsayawa takara a jam'iyyar.

A watan Janairun 2021 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa kuma Shugaba Museveni yana fuskantar gagarumin kalubale daga wajen dan majalisar dokoki na bangaren adawa, Robert Kyangulanyi wanda aka fi sani da Bobi Wine.

Ranar Laraba ne Mr Wine ya kaddamar da wata sabuwar jam'iyyar siyasa mai suna National Unity Platform Party kuma yana samun goyon baya sosai daga wurin matasa.

Masana na ganin Mr Museveni, wanda tsohon dan tawaye ne da ya hau mulki a 1986, yana so ya yi koyi ne da wasu fitattun shugabannin kasashen Afirka da suka rika mulki har sai da rai ya yi halinsa ko kuma aka tumbuke su daga kan mulki.

A halin da ake ciki dai, wasu shugabannin da suka dade a kan mulki sun hada da Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru.

Mr Biya, mai shekara 85 a duniya, ya hau mulki tun shekarar 1982.

A shekarar 2018 Shugaba Biya ya lashe zaben kasar a karo na bakwai a wani yanayi da mutane da dama ba su fita kada kuri'a ba da kuma tsangwamar masu kada kuri'a da aka dinga yi.

Masana na ganin nacewar da shugabannin Afirka ke yi na ci gaba da mulki ta hanyar sauya kundin tsarin mulki domin ya ba su damar sake tsayawa takara yana yin illa sosai ga tafiyar da harkokin kasashen.

Kazalika suna ganin hakan ne yake dada haifar da kama-karya da murkushewar da za ta kai ga hana 'yan kasa fadin albarkacin bakinsu.

Sai dai masu goyon bayan irin wadannan shugabannin na ganin dadewarsu a kan mulki tana taimakawa wajen wanzar da mulki mai dorewa da alkibla ga kasashen.