Uganda: An kashe mutun 16 a zanga-zangar kama Bobi Wine

A kalla mutun 16 a ka kashe a cikin kwana biyu na zanga zanga a Uganda, bayan da hukumomi su ka kama sanannen mawakinnan da ke takarar shugaban kasa wato Bobi Wine.

Rundunar yan sanda ta kuma tabbatar da jikkatar karin mutun 65 da kuma tsare wasu 350.

To sai dai ta ki ta yi bayanin yadda lamarin ya faru.

Wannan ne rikici mafi muni da ya auku a Kampala tun bayan tsayar da Bobi Wine takarar shugabancin kasa.

An kama Robert Kyagulanyi da a ka fi sani da Bobi Wine ne a ranar Laraba saboda keta dokar kullen Korona da a ka kakaba a fadin Uganda.

Mawakin mai shekaru 38 na fuskantar laifin hada taron jama'a duk da dokar kullen da a ka kakaba, bayan da ya hada gangamin yakin neman zabe a gabashin kasar.

Hakan ya sa hukumomi su ka tsare shi bisa laifin karya doka.

To sai dai yan adawa sun ce hukumomin suna nuna son kai wurin amfani da dokar, ganin cewa shugaba Museveni na gudanar da gangamin siyasar kwatankwacin irin wanda su ke shiryawa amma ba a kama kowa ba.

Bobi Wine na cikin jerin yan takara 11 da za su fafata da shugaba mai ci Yoweri Museveni, wanda ke kan karagar mulki tun a shekarar 1986.

Za a gudanar da babban zaben na Uganda ne a ranar 14 ga watan Janairun 2021.