Gwamnatin Netherland ta sauka kan baɗaƙalar damfara dagane da walwalar yara

After a Friday cabinet meeting the Dutch leader cycled to the palace to submit the government's resignation to King Willem-Alexander

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bayan taron majalisar ministocinsa shugaban Netherlands ya tafi fada a kan keke don sanar da Sarki Willem-Alexander murabus ɗin gwamnatinsa

Gwamnatin Mark Rutte ta yi murabus bayan an yi kuskuren zargin dubban iyalai da damfara kan tsarin kula da walwalar yara ƙanana kuma aka ce musu su mayar da kuɗaɗen da aka biya su.

Iyalai sun fuskanci "kurakurai daban-daban, kamar yadda ƴan majalisar suka yanke hukunci, inda jami'an tattara haraji da ƴan siyasa da alƙalai da ma'aikatan gwamnati suka bar su ba su da wani kataɓus.

Da dama daga waɗanda lamarin ya shafa sun fito ne daga waɗanda asalinsu ƴan ci-rani ne, kuma ɗaruruwansu sun faɗa mawuyacin halin tattalin arziki.

Mista Rutte ya sanar da sarki murabus din nasu.

"An bayyana mutanen da ba su ji ba su gani ba a a matsayin masu laifi kuma an tarwatsa musu rayuwa," kamar yadda ya shaida wa manema labarai, yana mai ƙarawa da cewa majalisar ministocinsa ce ke da alhakin kuskuren da aka yi. Kuma dole kusukuren ya tsaya a nan."

Wata uwa da a 2013 aka nemi ta mayar da euro 125,000 Dulce Gonçalves Tavares ta ce matakin ya jefata ita da yaranta cikin matsala.

"A matsayina na mara miji da ke kula da yara uku masu shekara takwas zuwa 11. Na shiga cikin matsanancin halin rashin kuɗi, kun san me? A wasu lokutan ni da ƴaƴana mu kan kwana ba mu ci abinci ba.

1px transparent line

Matakin na "bai ɗaya", da aka ɗauka a wajen taron majalisar minisoci a Hague, ya zo ne lokacin da ake tsaka da annobar korona.

An ayyana dokar hana fita Netherlands sannan minsitoci na duba yiwuwar ɗaukar tsauraran matakai don daƙile yaɗuwar cutar.

Gwamnatin za ta ci gaba da aiki a matsayin ta riƙon ƙwarya su tunkari cutar, har zuwa lokacin da za a yi zaɓen ƴan majalisa a watan Maris, amma ministan Tattalin arziki Eric Wiebes ya sauka nan take, saboda rawar da ya taka a badaƙalar.

Da aka tambaye shi ko murabus din na jeka-na-yi-ka ne, Mista Rutta ya nuna sam ba haka ba ne.

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Netherlands ta ajiye aiki ba a wani mataki na ɗaukar nauyi bai daya.

A shekarar 2002, gwamnatin ta ajiye aiki bayan wani rahoto ya zargi ministoci da sojoji da rashin hana yi wa Musulmai kisan kiyashi a Srebrenica lokacin yaƙin Bosniya a 1995.

2px presentational grey line

Me ya faru?

Sharhi daga Anna Holligan Wakiliyar BBC a Hague

An bayanna iyaye a matsayin ƴan damfara kan ƙananan kura-kurai kamar rashin sanya hannu a kan takardu, sannan aka tilasta musu mayar da maƙudan kuɗaɗe da gwamnati ta ba su don kula da yara, alhali ba su da wata hanyar da za a saurare su. Kamar yadda wani ƙaramin minista da ya yi murabus ya bayyana, gwamnati ta nuna musu fin ƙarfi.

Hukumomi sun jefa rayuwar iyalai da dama cikin ƙunci har suka zama "abokan gabar jama'a".

Mutane da dama sun ɓata da abokan zamansu, wasu sun rasa gidajen zama, iyaye mata sun ringa bayyana takaici cikin kuka saboda halin matsin tattalin arziki da matsananciyar damuwar da suka shiga bayan jami'an haraji sun sa su a gaba.

A bara, ofishin tattara haraji ya bayyana cewa an tsananta wa mutane 11,000 kawai saboda suna da takardar zama ƴan ƙasashe biyu.

Hakan ya ƙara ƙarfafa zargin da tsurarun ƙabilu ke yi a Netherlands cewa da jami'an gwamnati ne suke iza wutar nuna musu wariya.

The new ministers and state secretaries of the cabinet Rutte III pose for a group photo with King Willem-Alexander (C) and Prime Minister Mark Rutte at Palace Noordeinde in The Hague, Netherlands on October 26, 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun 2017 gwamnatin Rutte III ta hau mulki kuma za ta iya komawa ta kafa wani sabon ƙawancen bayan zaɓe

Sai dai yayin da ake kallon matakin a matsayin na sanin ciwon kai - suka sadaukar da muƙami don tabbatar da gazawar gwamnati - za a iya fassara murabus ɗin a matsayin kare kai da gwamnatin Rutt ta yi, don kaucewa shan kaye a ƙuri'ar yankan ƙauna daga ƴan majalisa a makon gobe.

2px presentational grey line

Me iyayen da aka zarga bisa kusukure suka ce?

Badaƙalar ta fara a 2012 kuma adadin iyayen da abin ya shafa za su iya kaiwa 26,000. Wasu sun fito fili sun yi kira ga gwamnnati da ta ti murabus, suna masu cewa sun fitar da rai cewa gwamnatin za ta iya gyara tsarin.

Wata uwa a yanzu haka na fuskantar buƙatar jami'an haraji suka nemi ta biya euro 48,000.

Ta yi ƙoƙarin yi wa hukumomi bayani cewa an yi kuskure, sai dai hukumomi a lokacin sun dage cewa ba a kudaden da ake bai wai yara ne kawai aka yi damfara ba, lamarin ya haɗa da wasu kudaden.

An biyo ta bashin kuɗin haya sannan kamfanin lanatarki na ƙin ba ta wutar lantarki. A ƙarshe dai ta rasa aikinta kuma ba ta samu wani ba domin ana kallonta a matsayin ƴar damfara.

Ta samu matsala da ɗanta yayin da ta ringa fuskantar matsin lamba.

Me zai faru nan gaba?

Jam'iyyar Mista Rutte mai sassaucin ra'ayin ta VVD tana samun nasara sosai a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a, don haka a zaben da za a yi ranr 17 ga watan Maris za a iya sake zabar gwamnatin da zai jagoranta. Tuni dai ya jagoranci gwamnati har sau uku tun daga 2010.

Duk da yake da farko ya nuna rashin amincewa da murabus ɗin ministocinsa, lamarin ya zama tilas tun bayan da jagoran hamayya Lodewijk Asscher ya yi murabus ranar Alhamis saboda badaƙalar.