Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jami'an tsaro sun kwashe Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna cikin dare
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami'an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.
Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin.
"Da misalin 12:00 na dare Sojoji da Ƴan sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren," in ji shugaban makarantar.
Ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa aka kama almajiran ba, amma tun bayan rufe makarantu lokacin ɓullar korona a karon farko, tun lokacin aka sallami ɗaliban makarantar, amma a cewarsa, waɗanda aka kama a yanzu waɗanda suke zaune a gidan Sheikh Dahiru ne ba wai waɗanda suka taso suka zo daga wani gari ba.
"Ba za mu iya tantance ko almajirai nawa aka ɗiba ba, domin cikin dare aka zo aka kwashe su," in ji shi.
Ya kuma bayyana mana cewa sun yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu damar magana da su ba.
Amma ko da BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kaduna, Manjo Garba Yahaya Rimi, shugaban hukumar kula da ababan hawa da muhalli ta jihar Kaduna, KASTELEA, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar korona a jihar ya bayyana cewa kai samamen na daga cikin matakan da suka fara ɗauka na daƙile annobar korona.
Ya kuma bayyana cewa wannan matakin ba wai ya tsaya bane kan makarantar Dahiru Bauchi kaɗai, inda ya ce ya shafi duka ƙananan hukumomi 23 ne na jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ɗalibai 140 suka kwasa daga makarantar kuma an ajiye su sansanin alhazai na jihar Kaduna inda ake tantance su, inda ya ce akwai wasu daga cikin almajiran da suka fito daga ƙasashe kamar Nijar da Chadi.
Gwamnatin ta ce idan aka gama tantance almajiran, waɗanda suka fito daga wasu jihohi za a miƙa su ga gwamnonin jihohinsu, na jihar Kaduna kuma za a miƙa su ga ciyamomi na ƙanan hukumomi, ɗaliban ƙasar waje kuma za a miƙa su ga hukumar shige da fice ta Najeriya.
Ko a bara sai da gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da yaɗa korona.
A lokacin, har sai da wannan lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin Kaduna da Kano inda Kaduna ke zargin almajiran da ake kai wa jihar da Kano ke kai korona jihar.
Hakan ya biyo bayan wasu almajirai 65 da aka kai su Kaduna daga Kano gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar korona.