Brexit: Boris Johnson ya yaba kan ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai

Tarayyar Turai da Birtaniya sun cimma matsaya kan huldar kasuwanci bayan kasar ta fice daga tarayyar, lamarin da ya kawo karshen wata da watannin da aka kwashe na rashin amincewa game da damar kamun kifi da wasu harkokin kasuwanci.

A taron manema labaran da ya gudanar a fadar Downing Street, Boris Johnson ya ce: "Mun sake dawo da damar da muke da ita a kan dokokinmu da makomarmu."

Firaiministan ya kara da cewa ko da yake an yi "zazzafar muhawara" amma hakan yana "da kyau ga daukacin Turai, abin da zai samar da ayyuka da kuma zaman lafiya."

Shugabar majalisar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce yarjejeniyar "tana cike da adalci da daidato".

A taron manema labaran da ta gudanar a Brussels, shugabar majalisar Tarayyar Turai ta ce: "Wannan hanya ce doguwa mai sarkakiya amma mun kulla yarjejeniya mai kyau wadda za mu iya nunawa.

"Yarjejeniya ce da aka kulla cikin adalci da daidaito kuma abu ne da ya dace da bangarorin suka yi."

Ta kara da cewa yanzu "lokaci ne da ya kamata a yi duba domin gaba" kuma Birtaniya za ta ci gaba da kasancewa "ƙawar da aka amince da ita".

Za a kwashe shekara biyar kafin a samu sauyi game da damar kamun kifi, in ji ta.

Ta kara da cewa za a ci gaba da hada gwiwa kan lamuran da suka hada da sauyin yanayi, makamashi da sufuri.

A wata sanarwa, fadar Downing Street ta ce: "Mun sake dawo da damar da muke da ita kan kudinmu da iyakokinmu da dokokinmu da cinikayyarmu da kuma ruwan da ake kamun kifinmu."

A yayin da take jaddada taken yakin neman zaben Mr Johnson, fadar ta kara da cewa "mun aiwatar da Brexit".

Mr Johnson ya wallafa hotonsa a Twitter yana murmushi inda ya nuna dan yatsansa a sama.

Babu abin da zai dawo da asarar da muka yi

Mr Johnson ya ce yana fatan majalisar dokokin Birtaniya za ta tuna ranar 30 ga watan Disamba ta kada kuri'a kan batun - akwai bukatar amincewar majalaisar Tarayyar Turai.

Jam'iyyar hamayya ta Labour Party - wadda ake tsammani za ta goyi bayan yarjejeniyar - ta ce za ta fitar da martaninta "idan lokaci ya yi".

Nan da kwanaki masu zuwa ne ake sa ran fitar da cikakken bayani kan yarjejeniyar.

Shugaban gwamnatin yankin Wales Mark Drakeford ya ce kulla yarjejeniyar ya fi da a ce ba a kulla ta ba amma ya soki lokacin da aka kulla ta wato mako daya kafin ficewar Birtaniya daga kasuwar Turai da kuma kungiyar hukumar yaki da fasa-kauri ta Turan.

Shugabar gwamnatin yankin Scotland Nicola Sturgeon ta ce: "Birtaniya tana ficewa daga Tarayyar Turai ne ba tare da Scotland tana so ba - kuma babu wata yarjejeniya da za a kulla wadda za ta dawo asarar da muka yi sakamakon ficewar.

"Lokaci ya yi da za mu nemi mafitarmu a matsayinmu na kasar Turai mai 'yancin kanta."