Brexit: Ina aka kwana tsakanin Birtaniya da EU kan Brexit?

    • Marubuci, Daga Chris Morris
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reality Check correspondent, BBC News

Ana cigaba da tattaunawa kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, duk da hasashen da ake yi cewa tattaunawar ba za ta yi nasara ba.

Sai dai tattaunawa kan Brexit na da iyaka game da nasarar da tattaunawar da ake yi a Brussels za ta samar.

Yanzu maganar siyasa ake yi - kuma lokacin kammala tattaunawar a karshen wata na kara kurewa.

Ina muka tsaya?

Birtaniya na neman sake rubuta yarjejeniya kan Ireland da Arewacin Ireland da ke cikin jarjejeniyar ficewar - daga cikin jarjejeniyar ficewar da tarayyar Turai da gwamnatin Birtaniya suka yi a lokacin Firai minista Theresa May.

Da farko Birtaniya ta dage sai an yi watsi da maganar rashin tsaurara matakai a iyakar Birtaniya da Tarayyar Turai ta yankin Yammacin Ireland wato 'backstop' a turance.

Kokarin Birtaniya na maye gurbin wannan zai sanya Yammacin Ireland wadda ba ta cikin Tarayyar Turai a cikin kasuwar kayayyakin gona da masana'antu ta bai-daya ta Tarayyar.

Hakan na nufin za a sammu sassauci a kan iyakar kudanci da arewaci (tsakanin Tarayyar Ireland da Arewacin Ireland). Amma za a samu dokokin shiga da ficen kaya tsakanin gabashi da yammaci (tsakanin Birtaniya da Arewacin Ireland).

Kamfanoni da masana'antu da dama na sukar wannan bukatar da Birtaniya ta mika a matsayi mafi muni ga bangarorin.

Tarayyar Turai ta ce tana tausaya wa kamfanoni dake bangarorin iyakokin Irelan da za su koma a cikin wani yanayi mai wuyar sha'ani na gudanar da kasuwanci.

Amma akwai yiwuwar karuwar sabani kasancewar tana neman a kammala kulla yarjejeniyar sannan ba ta son a ga laifinta idan aka kara cimma daidaito.

Masu shiga tsakani na EU sun fahimci cewa sakamakon dokokin EU, yanzu Birtaniya na neman kafa wata kasuwa ta bai-daya, baya ga wasu dokokin.

Amma EU ta bayyana wasu muhimman batutuwa kuma ta yanke shawarar cewa ba zai yiwu yarjejeniyar da Birtaniya ta gabatar a yanzu ta zama sharadin kulla yarjejeniyar ba.

Shige da ficen kaya fa?

A nan gizo ke saka.

Birtaniya na neman a rika binciken kaya daga iyakokin Ireland na kan tudu ta amfani da fasaha amma banda masu kananan sana'o'i da amintattun tsare-tsaren cinikayya.

Amma hakan na nufin EU ta amince tun kafin lokacin cewa daga cikin alamun shiga yarjejeniyar a hukumance shi ne za a daina bincikar kaya a kan iyakar tun kafin EU ta san ko bukatun Birtaniya masu yiwuwa ne.

Amma EU ba ta yarda da hakan ba.

Hakan kuma na nufin sai an sake kulla yarjejeniyar kasa da kasa kan safarar kaya da nufin kauce wa bukatar binciken takardu a kusa ko kan iyakoki.

Hakan na kuma nufin EU za ta yi sabbin dokoki da za su tsame Birtaniya daga dokokin EU kan ayyukan safarar kaya a Arewacin Ireland. EU na ganin hakan zai kawo barazana ga nagartar tsarin tattalin arzikinta - na kawancen ayyukan kwastan da kasuwancin bai-daya.

Birtaniya na kira ga EC ta zurfafa tunani. Amma EU ba ta ganin yiwuwar ci gaba da zaman iyakokin Ireland a bude yadda suke a yanzu, matukar Arewacin Ireland ba ta daga cikin Tarayyar Turai.

Tana cewa shirin Birtaniya ya dogara ne a kan fasahar da ba a taba amfani da ita a iyakar wata kasa ba a duniya.

Amincewa fa?

Wannan ma wata matsala ce.

Birtaniya ta ce ka da a yi zaton Arewacin Ireland za ta yarda da wasu dokokin da ba ta da ta cewa a kai, sai idan tun da farko ta riga ta amince.

Amma hanyar da take bukata domin amincewa ya ba wa wani bangare, wato kawayenta da Democrat, ikon hawa kujerar naki a kan kafa yankin Ireland na bai-daya a yankin, da kuma ba su damar hawa kujerar naki a duk bayan shekara hudu kan cigaba da wanzuwar yankin.

Babu tabbaci ko a nan gaba na batun amincewa za ta haifar da sabbin dokokin shige da ficen kaya - amma musabbabin yarjejeniyar ranar Good Friday da ta taimaka ta kawo zaman lafiya a Arewacin Ireland shi ne babu wanin bangare da za ta iya hawa kujerar naki a kan wani bangare na yarjejeniyar.

So, if a method could be found to seek the regular consent of all parties in the Republic of Ireland also, for post-Brexit trading arrangements, that could provide a way forward.

Saboda haka idan aka gano wata hanyar neman amincewar dukkan bangarorin jamhuriyar Ireland kan yarjejeniyar cikinikayya bayan Brexit, hakan zai samar da mafita.

Duk da cewa bangarensu za su bukaci a kira shi haka, hakan zai zama backstop mai takaitaccen lokaci.

Sauran yarjejeniyar da aka kulla tsakanin EU da gwamnatin Theresa May, wanda a baya Boris Johnson ya rika suka za su ci gaba da aiki.

Ko da yarjejeniyar za ta kullu a karshen lokaci, sai Fira ministan ya amince da bangarorin yarjejeniyar da a baya yake adawa da su.

Me ya rage?

Kwanaki masu zuwa na da muhimmanci.

Babu bangaren da ke so a dauke shi a matsayin wanda ya fice daga yarjejeniyar saboda sun san za su bukaci su sake cigaba da tattaunawa.

Wani lokaci sai daga karshe ake cimma yarjejeniya, ba zato ba tsammani.

"Ina ganin za a kulla yarjejeniyar," a cewar babban mai shiga tsakani na EU Michel Barnier. Ya ce, "da wuya, amma zai iya yiwuwa."

Amma siyasa a dukkan bangarorin, musamman Birtaniya, na iya sa a kasa cimma matsaya a shirin kulla yarjejeniyar.