Hotuna masu ƙayatarwa na banɗaki a ƙasashen Rwanda da Madagascar

Babban burin mai ɗaukar hoto Elena Heatherwick shi ne na yin aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu, domin daukar hotunan irin rayuwar da jama'a ke yi da ganin ana amfani da hotunan da ta yi wajen kawo sauyi.

Kungiyar Water Aid ce ta ba ta damar yin hakan, inda ta ɗauki hotunan al'ummomin da ke rayuwa cikin kauyuka masu nisa a Rwanda da Madagascar, tare da rakiyar wata 'yar jarida Sally Williams.

Makewayi a Gitwa

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Al'ummar kauyen sun yi amfani da kwanon rufi wajen haɗa banɗakin da Theresia da 'yarta ke kewayawa
Theresia

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Theresia, mai shekara 80, bazawara ce da ke da yara uku, wanda ke zaune a Gitwa, a Rwanda.
1px transparent line

Sai dai hukumomi irin wadannan ba wai sun zo ne a dare daya ba.

Bayan ta kammala karatunta na aikin jarida, sai ta zama uwa kuma ta sanya ra'ayin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje a ranta, maimakon daukar hotunan girke-girke na shafukan abinci na Guardian.

Amma dagewa ta yi mata amfani, kuma daga karshe Majalisar Dinkin Duniya ta ba ta izinin daukar hotunan ungozomomi a Haiti.

Damar ta zo ne bayan da editan hoto na wata gasa da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, inda ta nemi mutane su gabatar da hoton wani da suke so.

Domitria

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Domitria, mai shekaru 54, na zaune ita kaɗai amma jama'ar Gitwa sun haɗu don gyara gidanta da kuma gina mata banɗaki. Ta ce: "Yana da kyau kwarai da gaske. Ina kula da shi ta hanyar tsaftace shi. da kuma share shi.
1px transparent line

Yayin da take kasar Haiti ta hadu da daya daga cikin ma'aikatan kungiyar bada agaji ta Water Aid, kuma nan take lamarin ya dame ta, cewa mutane biliyan biyu a duniya ba su da damar yin bayan gida mai zaman kansa.

Heatherwick ta fara tsara yadda zata ɗauki hotunan da suka fi dacewa da matsalar.

Yadda aka tsara bandakunan ne suka ba ta sha'awa, kuma ba da daɗewa ba ta yanke shawarar wannan shi ne abin da take son ɗauka.

Heatherwick da Williams sun yi niyyar tafiya zuwa kasashe da dama, amma korona ta hana su, don haka suka isa har zuwa Rwanda da Madagascar.

Makewayi a Ambatoantrano

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Makewayin Jean-Pierre ya nuna jajircewarsa wajen tsafta: yana da siminti, maimakon katako ga kuma wani rufin azara domin hana ƙudaje shiga.
Jean-Pierre da matarsa da ɗansu a Ambatoantrano

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Jean-Pierre, suna zaune tare da matarsa, Pierrette, da ɗansu a Ambatoantrano, da ke Madagascar. Lokacin da dansa ya kamu da cutar zawo mai tsanani shekaru bakwai da suka gabata, Jean-Pierre ya yanke shawarar canza abubuwa da gina banɗaki ga iyalinsa. "Ina bukatar in kare lafiyar mutane," in ji shi. "Ba kamar yawancin gine-ginen da ke ƙauyen ba, waɗanda ke fuskantar yamma, nesa da iska, na tsara banɗakina tare da ƙofar da ke fuskantar gabas, cikin iska."
1px transparent line

A Madagascar, kashi 90% na al'ummar kasar - sama da mutane miliyan 22 - ba su da bandaki mai kyau, kuma sulusin 'yan Ruwanda - mutane miliyan hudu - suna cikin irin wannan halin.

Heatherwick da Williams sun shirya kai ziyara ƙauyuka biyu inda abubuwa suka inganta sosai.

A cikin Ambatoantrano, wani ƙauye mai nisa a tsakiyar tsaunukan Madagascar, da ƙauyen Gitwa, a tsaunukan kudancin Ruwanda, kusan dukkanin magidanta yanzu suna da wurarensu.

Yayin da suka isa kowane ƙauye sai suka sayi itace, suka ɗauki hayar kafintoci domin taimaka musu wajen daukar hoton.

Toilet in Ambatoantrano

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Noely

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Noely, mai shekara 42, manomiya ce a Ambatoantrano. Bazawara ce mai 'ya'ya biyar mata da jikia.
1px transparent line
Toilet in Ambatoantrano

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, An gida makewayi Marie Lydia ne bayan da kusan kowa a ƙauye ya mallaki nasa makewayi
Marie Lydia

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Marie Lydia tana zaune tare da mijinta da ɗiyarta mai shekaru huɗu a Ambatoantrano. Ta ce samun nasu bayan gidan ya canza taimaka mata musamman a lokacina da take da ciki.
Athanasia

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Athanasia, 58, bazawara ce mai 'ya'ya takwas, nakasassa ce kuma ta dau lokaci a asibiti.
Toilet in Gitwa

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Jama'a ne suka gina mata bandakin na Athanasia, wanda aka gina a karkashin bishiya
Agnes da jikarta Diane

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Agnes da jikarta Diane
Makewayi a Gitwa

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Agnes ta ce: "Ina matukar farin ciki saboda ba sai na tattara ciyawa kowace safiya ba na sa a saman rufin."
Marie-Pierrette

Asalin hoton, Elena Heatherwick / WaterAid

Bayanan hoto, Marie-Pierrette, 38, tana zaune tare da dan uwanta a Ambatoantrano, Madagascar kuma ta yi asara mai yawa da barin ciki sau uku.
2px presentational grey line

Dukkanin wadannan hotunan mallakin Elena Heatherwick / WaterAid / People's Postcode Lottery ne.