Hotuna masu ƙayatarwa na banɗaki a ƙasashen Rwanda da Madagascar

Babban burin mai ɗaukar hoto Elena Heatherwick shi ne na yin aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu, domin daukar hotunan irin rayuwar da jama'a ke yi da ganin ana amfani da hotunan da ta yi wajen kawo sauyi.

Kungiyar Water Aid ce ta ba ta damar yin hakan, inda ta ɗauki hotunan al'ummomin da ke rayuwa cikin kauyuka masu nisa a Rwanda da Madagascar, tare da rakiyar wata 'yar jarida Sally Williams.

Sai dai hukumomi irin wadannan ba wai sun zo ne a dare daya ba.

Bayan ta kammala karatunta na aikin jarida, sai ta zama uwa kuma ta sanya ra'ayin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje a ranta, maimakon daukar hotunan girke-girke na shafukan abinci na Guardian.

Amma dagewa ta yi mata amfani, kuma daga karshe Majalisar Dinkin Duniya ta ba ta izinin daukar hotunan ungozomomi a Haiti.

Damar ta zo ne bayan da editan hoto na wata gasa da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, inda ta nemi mutane su gabatar da hoton wani da suke so.

Yayin da take kasar Haiti ta hadu da daya daga cikin ma'aikatan kungiyar bada agaji ta Water Aid, kuma nan take lamarin ya dame ta, cewa mutane biliyan biyu a duniya ba su da damar yin bayan gida mai zaman kansa.

Heatherwick ta fara tsara yadda zata ɗauki hotunan da suka fi dacewa da matsalar.

Yadda aka tsara bandakunan ne suka ba ta sha'awa, kuma ba da daɗewa ba ta yanke shawarar wannan shi ne abin da take son ɗauka.

Heatherwick da Williams sun yi niyyar tafiya zuwa kasashe da dama, amma korona ta hana su, don haka suka isa har zuwa Rwanda da Madagascar.

A Madagascar, kashi 90% na al'ummar kasar - sama da mutane miliyan 22 - ba su da bandaki mai kyau, kuma sulusin 'yan Ruwanda - mutane miliyan hudu - suna cikin irin wannan halin.

Heatherwick da Williams sun shirya kai ziyara ƙauyuka biyu inda abubuwa suka inganta sosai.

A cikin Ambatoantrano, wani ƙauye mai nisa a tsakiyar tsaunukan Madagascar, da ƙauyen Gitwa, a tsaunukan kudancin Ruwanda, kusan dukkanin magidanta yanzu suna da wurarensu.

Yayin da suka isa kowane ƙauye sai suka sayi itace, suka ɗauki hayar kafintoci domin taimaka musu wajen daukar hoton.

Dukkanin wadannan hotunan mallakin Elena Heatherwick / WaterAid / People's Postcode Lottery ne.