Haramta Black Friday da Hisbah ta yi a Kano ya ja hankalin ƴan Najeriya

Hisbah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Takardar gargaɗi da hukumar Hisbah ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta aika wa wata kafar yaɗa labarai kan batun Black Friday, ranar da kantina ke zabtare farashin kayayyaki, ta ja hankalin ƴan Najeriya.

An ta yawo da wata takarda mai ɗauke da sunan hukumar Hisbah ta jihar Kano a kafofin sadarwa na intanet, mai ɗauke da gargadi ga kafar yaɗa labarai ta Cool FM.

Sunan Black Friday ya samo asali ne shekaru da dama, kuma an daɗe ana bikin Black Friday a ƙasashe da dama inda manyan kantina ke ware ranar Juma'a domin gwanjon kayayyakinsu musamman yayin da shekara ke ƙarewa.

A cikin takardar mai ɗauke da kwanan wata 26 ga watan Nuwamba, hukumar ta bayyana damuwa da kuma koken da ta ce ta samu game da ayyana Juma'a a matsayin Black Friday wato "Baƙar Juma'a."

"Muna bayyana damuwa kan ayyana Juma'a a matsayin Black Friday, kuma ya kamata a fahimci yawancin al'ummar Kano Musulmi ne da suka ɗauki Juma'a babbar rana."

"Don haka Hisbah na son a daina kiran Juma'a Black Friday cikin gaggawa," a cewar takarar ta hukumar Hisbah.

Takardar ta kuma nuna cewa Black Friday barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar jihar Kano.

Wannan umurnin na Hisbah na haramta Black Friday na cikin batutuwa da aka fi tattaunawa a shafukan sada zumunta musamman a Twitter.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Wasu na ganin Black Friday biki ne na kasuwanci da bai shafi addini ba, bai kamata Hisbah ta ɗauki matakin ba.

Nasiru Salisu Zango ya bayyana ra'ayinsa inda ya ce shi bai ga illar kiran Juma'a Black Friday ba yana cewa: "Babban ɗakin da muke mararin ziyarta mu nemi albarka wato Ka'aba ko yaushe a rufe yake da baƙin ƙyalle, sannan kuma akwai wani Dutse Mai albarka wato Hajaral Aswad wanda shima baƙi ne, Aswad da kalmar Larabci tana nufin black wato baƙi."

@iamsardeeq ya ce: "Wannan tunaninsu wanda ba shi da nasaba da addini kawai suna amfani da addini."

@DrOlufunmilayo ya ce: "Black Friday" shi ne inganta tallace-tallace da bai wa mutane farashi mai. Yana taimakawa kasuwanci. Yana taimakawa talakawa. Haka kuma "kasuwar lahadi" ba ya da alaƙa da kiristanci, "Black Friday" ba ta da alaƙa da addinin Islama."

Sai dai @sunnyyon ya ce: "duk da ba ni goyon bayan Hisbah amma ina adawa da ayyana abu baƙi, domin ba daɗe ba da ƴan Najeriya suka fara bikin Halloween, wai ba za mu iya yin namu bukukuwan ba."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Yawanci dai mutane kan jira ranar Black Friday domin samun rahusar kayayyaki musamman masu sari da ke da ƙaramin jari.