Dalilai biyar da suka sa aka hukunta kafafen watsa labarai 716 a Najeriya

NBC

Asalin hoton, NBC

Hukumar da ke sanya ido kan kafafen watsa labaran Najeriya, NBC, ta bayyana cewa ta hukunta kafafen watsa labaran kasar 716 ne saboda sun keta wasu dokokin da ta gindaya musu.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton da take fitarwa bayan kowanne wata uku, wanda ta fitar a ranar Laraba.

Rahoton ya yi nazari ne kan laifukan da NBC ta ce kafafen watsa labaran sun yi tsakanin watan Afrilu zuwa watan Yunin 2020.

Rahoton ya nuna cewa a cikin kafafen watsa labarai 716 da aka hukunta, 22 (ko kashi uku cikin dari) su ne suka shafi cin su tarar kudi.

Ya kara da cewa kafafen watsa labarai 694 (kashi 97) an ja kunnensu kan watsa labaran batsa, da na siyasa, da kalaman batanci, da labaran da ba su tantance ba, da rashin iya aiki da tallace-tallace da kuma tangardar na'ura.

''Keta dokokin tallace-tallace shi ne babban abin da aka fi yi a wadannan watanni uku, inda ya samu kashi 51 na karya dokokin da aka yi, yayin da yada labarai game da ikirarin samo magungunan cutukan jima'i da kuma masu wa'azi suka dauki kashi 17 na keta dokokin watsa labarai," a cewar rahoton.

Rahoton na NBC ya kara da cewa rashin iya gudanar da aiki, musamman a gabatar da labarai da al'amuran yau da kullum "shi ne ya zo na uku a cikin keta wannan doka, inda suka dauki kashi 12 na dukkan keta dokokin da aka yi a watannin da rahoton ya zayyano."

Kazalika rahoton ya nuna cewa an yi hukunce-hukunce 22 kan kafafen watsa labarai 19 a duk fadin Najeriya a tsawon watannin uku inda aka kuma ci tarar su tsakanin N250,000.00 zuwa N300,000.00 kowannensu.

An yi hukunci bakwai daga ciki su ne sakamakon watsa labaran karya game da cutar COVID-19.

Sauran kafafen watsa labaran da aka hukunta kan wannan batu su ne Breeze FM, Lafia, Adaba FM Akure, Midland FM Ilorin, Royal FM Ilorin da kuma Wave FM Port Harcourt.

A cewar rahoton, an hukunta kafafen watsa labarai 10 bisa watsa labaran da ke ikirarin samar da magungunan manyan cutuka da kuma masu bayar da sa'a.

Kafafen watsa labaran da wannan hukunci ya shafa su ne: Sobi FM, Ilorin; EBS Radio, Benin; City FM Onitsha; FRCN (Voice FM) Nsukka; King FM, Ibadan; Fad FM, Calabar; Wazobia Max TV, Port Harcourt da kuma Radio Rivers, Port Harcourt.

Wasu masu suka na gani hukumar ta NBC tana hukunta wasu kafafen watsa labaran ne saboda sun watsa labaran da ba su yi wa gwamnati dadi ba, sai dai wani darakta a hukumar da ba ya so mu ambaci sunansa ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, tun kafin a bai wa kafafen watsa labaran lasisi akwai ka'idoji da aka gindaya musu kuma ana hukunta su ne idan suka keta wadannan sharuda.