Fyaɗe: Uwa ta roƙi a bi kadin ƴarta ƴar shekara 12 da magidanta 7 suka ci zarafi a Sokoto

Wata uwa ta nemi a bi mata haƙƙin ƴarta ƴar shekara 12 da ake zargin wasu magidanta bakwai da yi mata fyaɗe irin na karɓa-karɓa a birnin Sokoton Najeriya.

Koken uwar na zuwa ne adaidai lokacin da wasu lauyoyi da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan'adam ke ta ƙoƙarin ganin an yi adalci ga marainiyar ƴar shekara 12 da aka ci zarafi.

Sakin mutanen da ake zargin sun aikata fyaɗen daga zaman jiran shari'a, ya jefa fargaba, ganin mai yiwuwa tuhumar da ake yi masu ta shiririce, kuma ana yi wa yarinyar da mahaifiyarta shaguɓe.

Lamarin dai ya janyo wa marainiyar tsangwama da kyara, har ta kai mahaifanta sun dakatar da ita daga zuwa makaranta, kuma ba a bari ta fita waje.

A cikin watan Fabrairu aka yi wa marainiyar mai fama da matsalar ƙwaƙwalwa fyaɗe.

Tun bayan aukuwar wannan lamari har yanzu babu wata shari'a ko ƙwaƙƙwaran hukunci da aka ɗauka kan mutanen da ake zargi.

'Yadda aka ci zarafin ƴata'

Mahaifiyar marainiyar ta ce magidantan da suka ɓata mata ɗiyarta dukkaninsu babu wanda shekarun sa yake ƙasa da 30, akwai ma wanda ya haura 50 a cikin magidanta da ake zargi.

Ta ce ta ƙawar ƴar uwarta suka gane cewa lallai waɗannan magidanta ne suka aikata fyaɗen domin an shaida musu cewa a hanyar makaranta suke kiranta su ci zarafinta.

"Bayan na samu labarin cewa wasu suna kiranta, a lokacin sai na shirya zan kai ta asibiti domin a duba ta nan ne ta shaida mun cewa ga abin da ake mata."

Barazanar kisa

Mahaifiyar ta ce cikin masu mata fyaɗen akwai wanda ya yi wa ƴarinyar barazanar sai kasheta idan ta sanar a gida.

"Sannan yana mata duka sai kuma ya miƙa ta ga sauran mazan abokan juna, lokacin da aka kama mutum guda a cikinsu da yake duk sun san junansu sai suka rinka tona wa kansu asiri."

Ta ce, "da aka kai su kotu sai aka ce musu ba za a iya yanke hukunci yanzu ba, sai dai a tura su gidan yari zuwa lokacin da za a miƙa shari'ar ta su babban kotu".

"Sai dai kafin a je kotun an sake su daya bayan daya kuma sun ci gaba da yawo a cikin unguwa da tutiyar cewa shari'a ta watse babu batun kotu.

Daya cikinsu akwai wanda yake tsayawa a kofar gidana yana mana dariya ba tare da nuna wani tsoro ba."

Wane hali yarinyar ke ciki?

Marainiyar ƴar shekara 12 a cewar mahaifiyarta tana cikin tsangwama da kyara ganin cewa irin waɗannan mutane sun aikata mugun aiki amma babu matakin da aka ɗauka.

Babu wanda zai iya kare ta yanzu. Ta daina fita makaranta da zuwa ko ina ko leƙa ƙofar gida.

Akwai samarin da ke barazanar cewa manya sun aikata laifi babu abin da akai musu don haka hadari ne a gareta, in ji mahaifiyar.

Akwai fargabar da iyayenta ke nuna wa kan abin da zai iya faruwa ko halin da yarinya za ta iya faɗawa a nan gaba.

Me yasa aka saki mutanen?

Barris Mansur Muhammad Aliyu, shi ne lauyan da ke wakiltar mahaifiyar yarinyar da ake zargin an yi wa fyaɗe, ya ce mutum shida cikin bakwai da ake zargi sun amsa wannan laifi.

Lauyan ya ce bayan binciken ƴan sanda an naɗi hoton bidiyo a lokacin da mutanen ke amsa sun aikata wannan fyaɗe.

Sai dai ƙasa da wata biyu lokacin annobar korona an rufe kotuna don haka sai aka sake su.

Kuma bisa dokokin jihar Sokoton an tanadi cewa babban lauyan gwamnati na da kwana 21 idan an kai masa irin wannan takarda ya bayar da matsayinsa.

Sai dai Barista Mansur ya ce ba shi da masaniya ko takardar shari'ar ta kai gaban babban lauyan jihar wanda kuma shi ne kwamishinan shari'a.

Amma dai a cewar lauyan suna dako domin tuni an miƙa takardar ma'aikatar shari'a.

Me jihar sokoton ke cewa?

BBC ta tuntubi kwamishinan shari'ar jihar, Sulaiman Usman, wanda ya shaida mana cewa suna kan batun kuma za su bi kadun ƙarar don ganin ba a bar wani giɓi ba.

Matsalar fyaɗe abu ne da ya jima yana ciwa al'umomi daban-daban tuwo a ƙwarya musamman a arewacin Najeriya da a kullum alƙaluman cin zarafi ƙaruwa suke yi.

Masu fafutika da rajin kare haƙƙi da ma ɗaiɗaikun mutane sun jima suna gangami ganin an sanya doka mai ƙarfi da za ta hukunta masu irin wannan aika-aika.

Masana dai na ganin idan ba an tashi tsaye ba da kafa doka mai tsanani na hukunci kan fyaɗe to a kullum lamarin zai ci gaba da taɓarɓarewa ne.

Yanzu dai abin zuba ido a gani shi ne ko wannan marainiya da ire-irensu da ke koke da irin wannan cin zarafi za a bi kadi a ƙwato musu haƙƙinsu.

Wasu labaran masu alaƙa