Recession: 'Yadda karayar tattalin arzikin Najeriya ta jefa rayuwar iyalaina a cikin tasku'

Ƴan Najeriya na ci gaba da ƙorafi a kan mawuyacin halin da suke shiga saboda tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Wannan yanayi da ƙasar ke ciki ya sake tsunduma ta cikin karayar tattalin arzikin da aka shafe gwamman shekaru ba a shiga irinsa ba.
A ƙarshen mako ne, hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce tattalin arziƙin Najeriya ya faɗi da kashi 3.62 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, abin da ke nufin tattalin arziƙin ƙasar ya samu matuƙar koma-baya.
Halin da Najeriyar ta tsinci kanta ya jefa jama'a da dama cikin mawuyacin yanayi a inda mutane da dama suka rasa ayyukansu, wasu kuwa abincin da za su sanya a bakinsu na salati sai da siɗin goshi suke samu.
Wani magidanci Malam Muhammad Mu'azu, ya shaida wa BBC cewa, ya rasa aikinsa da yake yi a wani gidan burodi da ke Hadeja a jihar Jigawa wanda da shi ya dogara wajen ciyar da iyalansa.
Magidancin ya ce: "A da a lokacin da ayyuka ke tafiya daidai a gidan burodin da nake aiki rayuwata da ta iyalina sai son-barka, amma a yanzu da aka rufe gidan burodin saboda hauhawar kayayyakin da ake sarrafa burodin, abincin da za mu ci ni da iyalaina wahala yake ba mu".
Ya ce ba kowacce rana suke dora tukunya ba saboda babu, ga kuma yara waɗanda ba lallai ne su fahimci halin da ake ciki ba.
Mai gidan burodin ya shaida wa BBC cewa, ya rufe gidan ne saboda yadda farashin kayayyakin da ake sarrafa burodi kamar fulawa da suga da dai sauransu suka yi tashin gwauron zabi.
Mai gidan burodin ya ce ba sa samun wata riba sai ma faɗuwa da suke, kuma da cinikin da aka yi ake samu a biya ma'aikatan da ke musu aiki kamar Malam Muhammadu Mu'azu.
Ba wai masu gidan burodin ne kawai suka shiga matsalar rayuwa ba, jama'a da dama a Najeriyar ma na kokawa da halin matsin da suka shiga saboda yadda shi kansa tattalin arzikin kasar ya shiga matsala.
Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce koma-bayan da tattalin arzikin ƙasar ya faɗa a cikin karo na biyu a shekara biyar bai zo musu da mamaki ba.

Me ya janyo Najeriya ta shiga matsalar tattalin arziki?

Asalin hoton, Getty Images
Masana tattalin arziki dai na ganin akwai wasu abubuwa da suka janyo Najeriya ta fada cikin wannan ƙangi, ciki har da batun annobar korona wadda ta sa aka rufe wasu ɓangarori na tattalin arzikin ƙasa musamman harkar masana'antu a inda kasuwanci ya samu naƙasu.
Sai kuma abu na biyu shi ne matsalar da aka samu a ɓangaren sayar da man fetur a kasuwar duniya, inda farashin man ya ke kwan-gaba kwan-baya kuma har yanzu bai daidaita ba.
Faduwar farashin man fetir da aka samu a kasuwar duniya ta sa Najeriya ba ta samun kuɗaɗen shiga isassu wanda hakan ya janyo tattalin arzikin ƙasar ya ja baya.

Me ya kamata ayi don fita daga wannan ƙangi?
Masana tattalin arzikin sun ce dole ne sai gwamnatin tarayyar ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da babban bankin ƙasa don a ƙara samar da ayyukan yi, a samar da jari, sannan a taimaka wa ƙananan da manyan masana'antu, a bunƙasa harkar kasuwanci sannan kuma a samar da ababan more rayuwa.
Kuma dole ne a bunƙasa harkar noma don abubuwa su tafi yadda ake so.

Ƙarin haske
Bankin Duniya ya ce wannan shi ne koma-bayan tattalin arziki mafi muni da Najeriya ta tsinci kanta ciki a cikin shekara 36.
Ƙasa na shiga karayar tattalin arziƙi ne idan adadin arziƙin da take samarwa a ƙasar ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfaɗo ba.
A daidai lokacin da Najeriyar ke ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi, darajar kuɗin Najeriya ta ƙara raguwa idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe da ke gogayya da naira a kasuwannin duniya.











