Najeriya ta sake faɗawa cikin karayar tattalin arziƙi

Nigeria currency

Asalin hoton, Others

A hukumance, Najeriya ta sake faɗawa cikin halin karayar tattalin arziƙi, a cewar alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta fitar ranar Asabar.

Tattalin arziƙin ƙasar ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, a cewar National Beareu of Statistics (NBS).

Me karayar tattalin arziƙi ke nufi?

Ƙasa na shiga karayar tattalin arziƙi idan adadin arziƙin da take samarwa a ƙasar ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfaɗo ba.

A daidai lokacin da Najeriya ke ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi, hakan na nufin cewa darajar kuɗin Najeriya ta ƙara raguwa idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe da ke gogayya da naira a kasuwannin duniya.

Ta yaya hakan zai shafi 'yan Najeriya?

  • Ga 'yan kasuwa, wannan lamarin zai shafi kuɗin da suke samu. Haka kuma adadin kuɗin da suke kashewa domin gudanar da kasuwanci zai ƙaru, kuma akwai yiwuwar cinkin da suke yi zai ragu.
  • Gwamnati za ta waiwayi manyan ayyukan da take kashe kuɗi a kansu domin dakatar da su, hakan na nufin wasu za su iya rasa aikinsu.
  • Akwai yiwuwar manyan kamfanoni da ke sarrafa kayayyaki za su iya korar ma'aikata domin akwai yiwuwar su ma za su rage adadin abubuwan da suke sarrafawa duba da yadda yanayin kasuwar ke tafiya.
CLOTHES WEY DEM

Shin Najeriya ta taɓa samun karayar tattalin arziƙi?

Lallai Najeriya ta taɓa shiga cikin wannan hali, domin kuwa tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2016, tattalin arziƙin ƙasar ya ragu da kashi 2.06 cikin 100 bayan ƙasar ta shafe wata shida tattalin arziƙinta bai murmure ba.

Hakan ya faru ne saboda karyewar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Farashin mai ya faɗo daga dala 112 kan kowace ganga a 2014 zuwa 50 a 2016.

Alƙaluma sun nuna cewa faɗuwar farashin kuɗin Najeriya ya girgiza tattalin arziƙin ƙasar.