G20 ta yi gargaɗi kan samar da wadatacciyar rigakafin korona

Shugabannin ƙasashen duniyar da suka halarci taron ƙasashe 20 da suke da ƙarfin tattalin arziki a duniya wato G20, sun bukaci sauran shugabannin ƙasashen duniya da ke da arziƙi su tabbatar da cewa an samar da rigakafin cutar korona wadatacciya ta yadda za ta iya kai wa ga ko ina a faɗin duniya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta buƙaci sauran shugabannin da su sanya ƙarin kuɗaɗe wajen samar da rigakafin a wadace.

Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron, ba a barshi a baya ba wajen jan hankalin sauran shugabannin a kan taimakawa don a samar da rigakafin a wadace ta yadda za ta isa dukkan ƙasashen da ke faɗin duniya.

Emmanuel Macron, ya ce kai rigakafin cutar ga ƙasashen kaɗai ba zai wadatar ba, dole a samar da wani tsari na kula da lafiya a matakin farko ga ƙasashe matalauta don su jima suna cin moriyar tsarin kula da lafiya a matakin farko.

Mr Macron ya ce, duk wani ƙoƙari da za su yi don tabbatar da wadatuwar rigakafin cutar ta korona ga irin waɗannan ƙasashe ba zai wadatar ba, dole ne sai sun ƙarfafa ko inganta tsarin kula da lafiyar ƙasashen a matakin farko.

Ya ce, wannan shi ne dalilin da ya sa dole akwai buƙatar ƙara zuba jari a ɓangaren tsarin kula da lafiyar ƙasasashen a matakin farko tare da tabbatar da an inganta tsarin.

Rahotannin sun bayyana cewa shugaba Trump na Amurka ya ƙauracewa taron wanda aka yi a kan yadda za a tunkari annobar korona.

Kafofin yaɗa labaran Amurka sun rawaito da nuna hotunan Trump yana buga ƙwallon golf adadai lokacin da ake wannan taro.

Ƙasar Saudiyya ce ta karɓi baƙwacin taron da aka gudanar kai tsaye ta intanet.