'A kalla sai baɗi' za a rabu da cutar coronavirus - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa za ta ci gaba da yakar kwayar cutar korona a kalla har zuwa tsakiyar shekara mai zuwa ganin cewa masu kamuwa da cutar sun zarce miliyan ɗaya.

A ranar Juma'a ƴan ƙasar fiye da 40,000 sun kamu da cutar inda mutum 298 kua suka mutu. Sauran ƙasashe kamar Rasha da Poland da Switzerland ma sun ce alƙaluman masu cutar sun yi tashin da basu taɓa yi ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tashin da cutar ke yi a nahiyar Turai na da tasiri matuƙa ga yadda za a yaƙi ƙwayar cutar.

Hukumar ta buƙaci a ɗauki matakan gaggawa domin kaucewa yanayin da zai dagula wa asibitoci damar iya kulawa da masu cutar.

Yawan masu cutar a Turai ya ninka har ma da ƙari cikin kwana 10 da ya wuce, kuma nahiyar na da mutum miliyan 7.8 da suka kamu inda kimanin mutum 247,000 kuma sun mutu.

"Watanni masu zuwa za su zama masu tsauri sannan wasu ƙasashen na kan hanyarsu ta fada wa cikin matsalar rashin iya magance matsalar nan ba da jimawa ba", inji Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya.

A fadin duniya akwai fiye da mutum miliyan 42 da ke dauke da cutar, inda mutum miliyan 1.1 kuma sun riga mu gidan gaskiya.

Shin me ke faruwa a Faransa?

Yayin wata ziyara da ya kai wani asibiti a yankin Paris, Mista Macron ya ce masana kimiyya na gaya masa cewa sun yi amanna cutar "za ta kasance tare da mu har zuwa tsakiyar baɗi".

Amma ya ce babu wanda ya san ko za a sake kulle jama'ar kasar a gidajensu kawo yanzu.

Amma akwai dokar hana fita cikin dare da ta fara aiki kuma ta shafi a kalla kashi biyu cikin uku na kasar - mutum miliyan 46 ke nan - daga daren Juma'a har nan da mako shida mai zuwa.

Sfaniya ma na fuskantar irin wannan jarabawar

A farkon wannan makon hukumomi a Sfaniya suka sanar da ƙasar ce ta farko da adadin masu cutar suka zarce miliyan ɗaya - amma ranar Juma'a Firaminista Pedro Sánchez ya ce 'ainihin yawan wadanda suka harbu da cutar' sun zarce miliyan uku.

Mista Sanchez ya bukaci ƴan ƙasar da su nuna "juriya, su bayar da tazara", amma bai bayyana wasu sabbin matakan yaki da annobar ba.

Wata dokar hana fita da aka ƙaƙaba wa Madrid - wanda jami'an birnin suka bijire wa - zai ƙare nan da ranar Asabar, kuma za a maye gurbinsa da hana 'yan gida daya taruwa a wani wuri da ke wajen gidansu daga 12 na dare zuwa 6 na safe.