ASUU and FG: Ɗaliban Najeriya sun fusata a shafin Twitter kan yajin aiki

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ta umarci dukkan malaman jami'o'in da su nemi wata hanya ta dogaro da kai saboda nuna halin ko in kula da ta ce gwamnatin ƙasar ta nuna game da biyan buƙatunsu.

Farfesa Haruna Musa, shugaban Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Najeriyar reshen Jami'ar Bayero ta Kano ya tabbatar wa BBC da batuna a wata hira ranar Laraba.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga iyaye da su kansu ɗaliban jam'o'in da ka da su sa ran yiwuwar koma wa makaranta a nan kusa.

ASUU ta kuma nuna damuwarta kan dakatar da biyan albashinsu har na tsawon watanni takwas.

Tun da farko dai a ranar Larabar ɗaliban Najeriya da dama sun wayi a fusace tun bayan wani shafin bogi na Ƙungiyar Malam Jami'o'i wato ASUU ya fitar da wata sanarwa inda ya buƙaci malaman na jami'o'in da su nemi wata hanya da za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

Sau da dama ƙungiyar ASUU ta sha fitar da sanarwa a rubuce inda take nesanta kanta da duk wani shafin bogi da ke wallafa saƙonni a madadinta.

Sai dai a wannan karon, ganin cewa ɗaliban jihohin Najeriya sun ƙagara su koma makaranta, kuma sun zaunu a gida kusan wata tara, ya sa suka fusata a shafin Twitter.

Hakan ya sa mau'du'in ASUU ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da aka wayi gari ana tattaunawa a shafin Twitter a ranar Laraba.

Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don saurarn cikakkiyar hirar Bilkisu Babangida da Farfesa Haruna Musa:

Me 'yan Najeriya ke cewa?

Wannan cewa ya yi yana ganin hauka ne a ce har yanzu ƙungiyar ASUU na yajin aiki, a cewarsa, duk da ya ɗora laifi a kan gwamnatin ƙasar, ya kuma ɗora laifin yajin aikin a kan ƙungiyar ta ASUU.

Wanda hakan ya sa yake saka alamar tambaya kan lamarin gaba ɗaya da cewa ta yaya za a ce an zauna kan teburin sulhu na watanni takwas ba tare da samun wata mafita ba?

Wannan kuma cewa ya yi sadaukar da rai da ASUU ke yi suna yi ne domin kawo ci gaba ga jami'o'in Najeriya. A cewarsa, 'ya'yan malaman, su ma jami'o'in gwamnati suke zuwa. Ya kuma yi ƙarin haske kan cewa albashin farfesa a jami'a bai wuce dubu 450 ba.

Shi kuma wannan cewa ya yi a yadda ASUU da gwamnatin tarayya ke tafiyar da abubuwa, wani zai iya tunanin cewa kyauta ake zuwa makaranta.

Ya kuma yi ƙorafin cewa da kuɗinsa yake biyan kuɗin makaranta amma suna jan aji kafin su yi hakan.

Sanarwar da ASUU ta fitar a baya

Ko a kwanakin baya sai da ƙungiyar ASUU ta fitar da sanarwa kan cewa akwai wasu shafukan sada zumunta da ke amfani da sunanta wurin yaɗa labaran ƙarya game da ita.

Ƙungiyar ta fitar da sanarwa a rubuce inda ta nisantar da kanta daga waɗannan shafukan inda ta ce ba ta da shafin sada zumunta ko ɗaya.

Tun a lokacin da ƙungiyar ta fitar da wannan sanarwar, sai da ta buƙaci jama'a da a kai ƙarar wannan shafin domin rufe shi.

Ina aka kwana kan batun ASUU da gwamnatin tarayya?

An shafe sama da watanni takwas a teburin sulhu domin magance matsaloli tsakanin ƙungiyar ASUU da gwamnatin Najeriya.

Rashin jituwa tsakanin ASUU da gwamnatin ta samo asali ne tun a lokacin Marigayi Umar Yar'adua inda ya yi musu wasu alƙawura waɗanda aka kasa cika musu.

Haka kuma sai waɗannan alƙawuran suka haɗu da babbar matsalar da ƙungiyar ke fuskanta a yanzu wadda ita ce ta tsarin biyan albashi ta IPPIS, inda malaman suka ce idan har gwamnati ba ta cire jami'o'i daga wannan tsari ba, ba za su janye yajin aikinsu ba.