Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
ASUU: Abubuwan da aka tattauna tsakanin ASUU da gwamnati
Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta amince ta biya ƙungiyar malaman Jami'oi ASUU naira biliyan 30 a tattaunawar da suka yi a ranar Alhamis.
Ana tunanin ɓangarorin biyu sun fahimci juna amma kuma hakan bai sa ɓangaren ƙungiyar malaman ya sanar da janye yakin aikin ba inda ƙungiyar ta sake amincewa su sake zama teburin tattaunawa da gwamnati.
Wata sanarwar da ma'aikatar ƙwadago ta fitar ta ce gwamnati ta amince ta fitar da kuɗi ga jami'o'in.
Sai dai kuma gwamnati ba dukkanin kuɗin za ta ba jami'o'in ba, za ta dinga fitar da su ne kaɗan-ƙadan tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022.
An shafe wata shida ɗaliban jami'o'i na zaman gida a Najeriya saboda yajin aikin na ASUU duk da ɗage dokar kulle da gwamnati ta yi.
Baya ga biliyan 30 da gwamnati za ta biya ASUU, bayanai sun kuma ce gwamnati za ta kashe naira biliyan 20 wajen farfaɗo da ɓangaren ilimi a wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yajin aikin na fiye da watanni shida.
Sai dai kuma kan batun tsarin albashi da ASUU ke jayayya da gwamnati akai, ɓangarorin biyu sun samu saɓani akai inda malaman Jami'oin suka ce sai dai a biya su albashin da suke bi ta tsarin albashin GIFMIS, yayin da kuma gwamnati ta dage kan tsarin IPPIS da ASUU ke adawa da shi.
Cikin wata sanarwa ASUU ta bukaci dukkanin mambobinta su ƙauracewa jami'an IPPIS da ta ce za a tura aikin rijistar malaman a jami'o'i daga ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.
Ƙaramin ministan ƙwadago Festus Keyamo ya faɗa a shafinsa na Twitter cewa za su yi ƙoƙarin shawo kan ƙungiyar ASUU kan batutuwa da dama ciki har da tsarin albashin IPPIS da malaman ke jayayya akai.
Tun da farko ASUU ta nuna cewa tsarin biyan albashin IPPIS, shi ne babbar matsalarta, kuma idan har gwamnati ba ta yi wani abu a kai ba, to malaman jami'oi ba za su janye yajin aikin ba, kamar yadda Shugaban kungiyar ta ASUU reshen Jami'ar Bayero Kano Farfesa Haruna Musa ya shaida wa BBC.