EndSARS: Femi Adesina ya gamu da fushin ƴan Twitter kan cewa Buhari ya cika cikakken Uba

Lokacin karatu: Minti 2

Wani rubutu da Femi Adeshina mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harakokin yaɗa labarai ya yi ya ja hankalin masu amfani da Twitter, inda ya kasance ɗaya daga cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya.

A cikin maƙalar da ya wallafa a ranar Juma'a mai taken "Ba mu da iyaye da yawa" kamar yadda ya saba rubutu duk ranar juma'a, Adeshina ya ce Shugaba Buhari ya nuna kamala irin ta uba a yayin zanga-zangar EndSARS da ta girgiza Najeriya a watan jiya.

Ya ce idan da Buhari bai yi haƙuri a matsayinsa na uba ba, da an shiga wani yanayi a Najeriya.

"Da yanzu zaman makoki muke idan da Buhari bai nuna dattukunsa na uba ba," in ji shi.

Haka kuma a cikin maƙalar ya ce akwai wasu da Buhari ke girmamawa da su suka tunzura masu zanga-zangar amma suka saɓe bayan ta rikiɗe ta koma rikici.

A cewar Adeshina - "Duk ta hanyar zanga-zangar EndSARS da ta koma tarzoma da tashin hankali da warwason kayan abinci da suka biyo baya, Shugaba Buhari ya nuna shi uba ne.

"Kuma duk da cewa akwai miliyoyin masu tsawatarwa a ƙasar nan, ba mu da iyaye da yawa. Shugaba Buhari shi ne kaɗai."

Waɗannan kalaman ne suka ja hankalin ƴan Najeriya a Twitter inda suka kama caccakar mai bai wa shugaban shawara.

@smart33hypertek ya ce - muna da masu tsawatarwa a ƙasar nan amma Buhari ya nuna shi uba ne, shin Femi Adeshina yana son ya faɗa muna cewa muna da shugabanni da yawa a Najeriya ne, Buhari kawai Uba ne?

@AishaYesufu ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar EndSARS ta adawa da rundunar ƴan sanda masu fashi da makami da aka rusa, tambaya ita ma ta yi.

Kenan wannan ne dalilin da ya sa aka bar ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan fashi masu satar mutane?

@OmoEyero ta ce Femi Adesina ba ya ƙara wata daraja ga fadar shugaban ƙasa.

A cikin rubutunsa Femi Adeshina ya ce ya kamata ƴan Najeriya su gode wa Shugaba Buhari saboda haƙurinsa da juriyarsa ga kuskuren wasu.

An shafe makwanni dubban ƴan Najeriya yawancinsu matasa na zanga-zanga a watan da ya gabata kan ƴan sanda da suke zargi da cin zarafi da azabtarwa wani lokaci da aikata kisa.