Wasiƙar ƴan Najeriya ga Buhari kan matsalar satar mutane

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Lokacin karatu: Minti 3

Taɓarɓarewar tsaro ya kasance babbar matsalar da ta dami ƴan Najeriya musamman a arewacin ƙasar.

Hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane domin ƙudin fansa, matsala ce da har yanzu aka kasa magancewa, inda ko a ranar Lahadi ɓarayi ƴan fashi sun tare hanyar hanyar Abuja zuwa Kaduna, suka sace mutane da dama bayan sun kashe wasu.

Ganin yadda batun ya ja hankalin ƴan Najeriya ya sa muka tambayi masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta cewa - wace shawara za su ba Shugaba Buhari kan yadda za a kawo ƙarshen matsalar tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna?

A shafinmu na Facebook mutum sama da dubu 234 suka ga sakon, an yi tsokaci kusan 4,000 cikin kasa da sa'a 24.

Yayin da wasu ke ɗora laifin ga gwamnatin Buhari, akwai wadanda suka ba shi shawara, da kuma masu yaba masa.

Wasu na ganin matsalar tsaron ba a iya hanyar Abuja zuwa Kaduna ake fama da ita ba, kusan ana fama da matsalar a jihohin arewa maso yammaci bayan matsalar Boko Haram a arewa maso gabashi.

Ga masu ba shugaban shawara suna ganin akwai buƙatar a ɗauki sabbin matakai da canza salo.

ra'ayin Facebook

Asalin hoton, Awwal Ahmad

@Nizam Mustapha ya ba shugaba Buhari shawarwari guda uku kamar haka:

1. Gwamnati ta karfafa samo bayanan sirri kan waɗanda ke da hannu acikin wannan ta'addancin, ina ne maboyarsu? Da wa suke mu'amala?

2. A ƙara yawan jami'an tsaro sannan a basu horarwa da kyau, a kuma wadata su da makamai na zamani masu inganci. A kuma wadata jami'an tsaro da albashi mai kyau da abubuwan walwala na more rayuwa

3. Kar ace za a tsaya jiran ƴanta'adan a kan titi kadai, a bisu har maɓuyansu a yi maganinsu.

Shi ma @Hamza Nuhu Dantani shawara ya ba shugaba Buhari kamar haka: " Shawara ta anan shine. Yakamata su shugaba Buhari ya ɗauki gagarumin mataki akan wannan al'amari. Ya dawo da martabar ƴan sanda musamman bangaren yaƙi da masu fashi da yan satar mutane."

"Kamar kungiyar da Dcp Abba kyari ke jagoronta (IRT), da kuma ƙungiyar Dcp Kolo ke jagoranra wato (STS).Wallahi tunda aka janyesu akan wannan hanyar sai wannan al'amari na masu garkuwa da mutane ya karfafa."

"Wannan lamarin yana son a dauki mataki mai inganci. Kuma yakamata buhari ya tsaya da kafafunsa ya saka jami'an tsaro su dauki mataki mai karko."

A nata ra'ayin kuma @Safiyyat Abdulhamid daga Kumasi Ghana cewa ta yi "maganar gaskiya gwamnatin Buhari ta gaza Samar da cikakken tsaro kamar yadda ya yi alkawarin Samar da tsaro a ciki da wajan Nigeria baki daya."

"Yanzu saboda Allah babbar hanya kamar Kaduna zuwa abuja amma ace babu tsaro,gaskiya ya kamata gwamnatin jahar Kaduna da gwamnatin Tarayya su yi iya iyawar su domin baza jami'an tsaro, Kuma abasu manya manya makaman aiki na zamani masu ban tsoro da razanar wa ga barayin daji,da kuma binciken kwakwaf akan musabbabin wannan lamarin da yake son ya gagari gwamnati."\

A shafin Instagram kuwa saƙon ya samu tsokaci sama da 200 kuma an so shi sau kusan 3500:

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Daga cikin masu tsokaci a Instagram, wasunsu sun ba shugaban shawara ya musanya manyan hafsoshin sojin ƙasar.

Wasu kuma na ganin akwai sakacin gwamnati da kuma rashin ɗaukar matakan da suka dace na shawo kan matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.

line

Ana fama da karuwar matsalolin tsaro a baya-bayan nan a Najeriya kuma gwamnati a lokuta da dama ta sha ikirarin cewa tana ci gaba da kokari na ganin ta fitar da Najeriya daga kangin rashin tsaron.

Al'ummar yankin arewa maso yammaci sun daɗe suna fama da matsalar satar mutane domin neman ƙudin fansa. Kusan lamarin ya fi shafar jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Kaduna.

Duk da rundunonin soji da aka kafa domin yaƙar ƴan fashin da kuma ikirarin hukumomin Najeriya na ɗaukar matakai amma har ana fama da ƴan fashin.

Baya ga tare hanyar Abuja zuwa Kaduna, a karshen makon nan, sai da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka shiga Kwalejin Nuhu Bamalli da ke wajen birnin Zariya, inda suka sace wani malami suka kuma harbi mutum ɗaya a hannu tare da sace 'ya'yansa biyu.

A garin Jangebe da ke Talatar Mafara a jihar Zamfara, al'ummar yankin sun ce sun kwana cikin juyayi na mutanensu sama da 30 da aka sace a kan hanyarsu ta komawa kauyukansu daga kasuwar Bagega a yammacin ranar Asabar.