Buhari ya nemi haɗin kan sarakuna don biya wa matasan Najeriya buƙatunsu

Buhari da Oni

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi goyon bayan masu sarautun gargajiya wajen ƙoƙarin gwamnatinsa na biya wa matasan ƙasar buƙatunsu.

A ranar Alhamis ne shugaban ya nemi hakan a wani taro da ya yi da masu riƙe da sarautun gargajiyar wanda aka yi a fadarsa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

''Mun ji koken-koken matasanmu da ƴaƴanmu kuma muna duba buƙatunsu,'' a cewar Shugaba Buhari.

Ana ganin shugaban ya shirya taron ne bayan da aka shafe makonni biyu matasa a ƙasar suna gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rundunar ƴan sanda mai yaƙi da fashi da makami ta Sars.

Matasan sun gabatar da wasu ƙarin buƙatun baya ga na rushe Sars wanda ta gwamnati ta biya musu ta hanyar rushe rundunar, sai dai duk da haka ba su janye daga tituna ba, lamarin da a ƙarshe ya rikiɗe zuwa rikici.

A yayin taron, Shugaba Buhari ya kuma jaddada cewa, ''Domin yin nasara a kan wannan muradi namu, muna son goyon bayanku da amfani da muryarku don taimakawa wajen isar da saƙonmu.

''Kusancinku da mutanen nan ne ya sa kuka fi dacewa da isar musu da saƙon da tabbatar da cewa sun samu martaninmu kuma ya yi tasiri,'' a cewar shugaban.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari ne zai jagoranci manyan jami'an gwamnati zuwa sassan ƙasar daban-daban ''inda za su tattauna da ku a wannan aikin. Daga nan zai kawo min rahoto kan ra'ayoyinku,'' in ji Buhari.

Wannan layi ne

Ƙashin bayan al'umma

Sarkin Musulmai Alhaji Sa'ad Abubakar ne ya jagoranci tawagar masu sarautun,

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Sarkin Musulmii Alhaji Sa'ad Abubakar ne ya jagoranci tawagar masu sarautun

Shugaba Buhari, ya bayyana rawar da masu sarautun gargajiyar ke takawa a matsayinsu na masu kula da kare martabar al'adu, sannan ya roƙe su da su riƙe amanar da aka dora musu tare da mayar da kowa nasu.

Ana ganin martabar da masu sarautun gargajiya ke da ita a idon al'umma ce ta sa shugaban ɗora musu wannan nauyi.

"Ina son na sake gode muku kan rawar da kuka taka wajen kwantar da hankalin matasa ta hanyar amfani da fasaharsu da kuma cikakken ikon da suke da shi. Idan har kuka tabbatar da zaman lafiya, to kun yi wa ƙasar nan babban aiki,'' kamar yadda ya ƙara da cewa.

Gyara kayanka

Buhari Sallau

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shugaba Buhari ya kuma yi gargaɗi cewa gwamnatinsa ba za ta bar kowa ko waca ƙungiya ta yi wa zaman lafiya barazana ko lalata ƙoƙarinta ba.

Sannan ya ce a yanzu haka ana ƙoƙarin magance ɓata gari daga cikin rundunar ƴan sandan ƙasar, tare da kawo sauyi a aikinsu ta hanyar inganta walwalarsu da yanayin aikinsu.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ne ya jagoranci tawagar masu sarautun, wadanda suka haɗa da Ooni na Ife, da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi da Sarkin Kano da Sarkin Fika da Tor na Tiv da shugaban sarakunan gargajiya na jihar Imo da sauran manayan masu sarautun gargajiya daga faɗin ƙasar.

Wannan layi ne