Girgizar ƙasa ta afkawa Turkiyya da Girka

Asalin hoton, Reuters
Masu aikin ceto a birnin Izmir na Turkiyya sun kwana suna hako bululluka masu ƙwari a cikin duhu domin lalubo wadanda ke da sauran numfashi bayan girgiza kasa ta afkawa Aegean a jiya Juma'a.
Magajin garin Izmir Tunc Soyer yace gine-gine 20 suka rushe, masu aikin agaji sun bada rahoton mutuwar mutane 20, dari 7 kuma sun samu rauni.
Girgizar kasar mai karfi maki 7 ta kuma lalata tsiribin Samos na Girka da ke kusa, da sanadi rayukan yara 2 bayan katanga ta rufta musu.
Guguwar ta kuma haddasa tumbatsar teku inda ruwa ya malala a tittuna unguwannin da ke kuda da tashar jirgi.
Guguwar ta kuma haddasa tumbatsar teku inda ruwa ya malala a tittuna unguwannin da ke kusa da tashar jirgi.
Da yake jawabi a Santanbul, shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya bayyana jaje da jimaminsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ya ce, "Ina so na mika tare da bayyana jimami na ga wuraren da iftila'in girgizar ya afkawa, Kazalika ina mika sakon ta'aziyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan iftila'i haka suma wadanda suka samu raunuka ina musu fatan samun sauki".
Girgizar kasar ta kuma lalata tsiribin Samos na Girka da ke kusa, tare da sanadin rayukan yara 2 bayan katanga ta rufta musu abinda Mr Erdogan ya ce firaministan kasar ta Girka ya yi masa tayin kawo wa Turkiyyan dauki.
Mr Erdogan ya ce, firaministan Girka ya kira shi koda ya ke suma girgizar kasar ta shafe su sai dai ba sosai ba.Ya ce suna mika godiyarsu ga Girka bisa tayin kawo musu dauki d ata yi koda yake na shaida masa cewa mun gode amma a yanzu bama bukatar taimakonsu.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu akwai 'yar mishkila a ciki a yan watannin baya-bayan nan saboda sabanin da suka samu a kan abin da ya danganci iko da ruwan da ka kan iyakokin kasar da ma sauran wasu albarkatun kasa da ke kan iyakokin kasashen biyu.











