Shugaban ƙasa ya kwanta asibiti kwanaki kafin zaɓe kan kundin tsarin mulki

Rahotanni daga Algeria sun bayyana cewa an kwantar da shugaban ƙasar Abdelmadjid Tebboune, a asibiti kwanaki kadan kafin zaɓen raba gardama kan fasalta kundin tsarin mulkin ƙasar.
An kwantar da shugaban ƙasar ne a wani asibitin soji da ke babban birnin Algeria.
A ranar Asabar ɗin data wuce ne shugaban ƙasar ya killace kansa na tsawon kwanaki biyar bisa shawarar da likitoci suka bashi na yin hakan.
Likitoci sun bashi shawarar ne bayan da aka samu mukarrabansa da kuma wasu kusoshi a gwamnatin ƙasar sun kamu da cutar korona.
Ofishin shugaban ƙasar ya sanar da cewa shugaba Abelmadjid wanda ke kwance a wani bangare na musamman a asibitin na samun sauki.
Sai dai kuma ba a bayyana cewa ko ya kamu da cutar korona ba ne.
Shugaba Abdelmadjid Tebboune, mai shekara 74, ya shaida wa al'ummar ƙasar cewa yana cikin koshin lafiya kuma zai ci gaba d agudanar da ayyukansu daga asibitin da aka killace sa.
Idan har aka tabbatar da ya kamu da cutar korona, to zai shiga cikin jerin shugabannin ƙasashen duniya da suka kamu da annobar korona ciki har da Donald Trump na Amurka da firaministan Birtaniya Boris Johnson da kuma shugaban Brazil Jair Bolsonaro.
Ana samun ƙaruwar wadanda suka kamu da cutar korona a Algeria a cikin makonni biyu da suka shuɗe lamarin da ya janyowa tattalin arzikin ƙasar matsala.
Akalla kusan mutum dubu 57 ne suka kamu da annobar a ƙasar da take da yawan mutane miliyan 44.
Haka kuma an samu mutum 1,930 da suka mutu bayan sun kamu da cutar ta korona a ƙasar.











