EndSARS: Yadda zanga-zangar ta sauya Najeriya har abada

Protesters at Lekki toll gate

Asalin hoton, Getty Images

Zanga-zangar da matasa suka yi ta kyamatar kisa da cin zalin da ƴan sanda ke yi a Najeriya ta haifar da wata gagarumar ƙungiya da ta girgiza masu mulki a ƙasar.

Bayan tashin-tashinar da aka yi ta mako biyu, editan BBC Hausa Aliyu Tanko ya duba mana inda aka dosa daga nan.

Wani gangami na zanga-zanga a tituna da wanda aka yi a shafukan sada zumunta ya bai wa matasan Najeriya wata kafa da ta haddasa rusa tsarin girmama na gaba da aka saba da shi a ƙasar.

Yayin da gangamin #EndSARS ya bazu ko'ina, a lokacin ne kuma bijire wa masu rike da madafan iko ya kunno kai a Najeriya.

Lalata fadar Oba ko kuma sarkin gargajiyar Iko da ake matukar girmamawa a Legas, ta kasance manuniya ga halin da aka faɗa.

Matasan da suka faɗa cikin fadar sun rika fatali da karagarsa kuma sun kwashe kayansa har ma sun yi wanka a cikin wurin nunƙayarsa.

Abin da ya samo asali daga zanga-zangar nuna rashin amincewa da wata rundunar ƴan sanda mai matuƙar bakin jini ta Special Anti-Robbery Squad (SARS), ya kasance wata hanyar da matasa za su huce fushinsu da mutanen da suka shafe gomman shekaru suna mulkin ƙasar, kuma suna buƙatar sauyi.

Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya taɓa yin gargadi a 2017 cewa "dukkammu muna zaune ne a kan tukunyar bam" game da al'amuran matasa.

Ya yi kalaman nasa ne kan matasan nahiyar baki ɗaya, amma sun yi daidai da abin da ke faruwa a Najeriya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'ummarta ya kai miliyan 200 kuma fiye da kashi 60 cikin 100 na al'ummar ƙasar 'yan ƙasa da shekara 24 ne da haihuwa.

Yawancin waɗanda suka kai munzalin yin aiki cikinsu ba su da aikin da ya dace su yi, kuma ba su da damar samun ilimin zamani.

A farkon wannan shekarar alƙaluman da gwamnati ta fitar na cewa kashi 40 cikin 100 na ƴan Najeriya na rayuwa cikin talauci.

'Ba kasafai aka saba shiga wannan halin ba'

Da farko waɗanda ke mulkin kasar a yanzu ba su fahimci abin da ke faruwa ba, inji Gimba Kakanda, wani mai gwagwarmaya kuma marubuci a wata hira da ya yi da BBC.

"Sun ɗauka zanga-zangar #EndSARS irin wadda suka saba gani a da ce, wadda matasan za su gaji su watse da kansu idan aka ƙi kula su."

Ya kara da cewa: "Wannan tunanin na masu mulkin kasar, wanda kana iya cewa na rainin wayon matasan ne, shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta yi sanyin tunkarar wannan gagarumin yunƙurin, kuma ya gigita su."

Bayanan bidiyo, Ta yaya ya kamata a warware batun EndSars?

Abin tambaya a nan shi ne, ina wannan gwagwarmayar za ta dosa?

Nasarorin da aka samu na yadda gwamnati ta yi saurin amsawa da buƙatun da masu zanga-zangar suka fitar - kamar rusa rundunar SARS da yin sauye-sauye ga aikin ƴan sanda - ya ba matasan Najeriya karfin gwiwar cewa za su iya kawo sauyi.

Kwananki kadan da fara zanga-zangar, masu fafutika cikin matasan sun samar da hanyoyi ga masu bukatar taimakon gaggawa. Sun kuma rika bayar da taimako a fannin shari'a ga masu bukata har ma sun kafa wata tashar rediyo.

Dukkan wadannan ayyukan sun samu ne ta hanyar tara kudade da suka yi ta amfani da fasahar sadarwa ta zamani da ake kira crowdfunding, matakan da aka rika kallo a matsayin yadda Najeriya ka iya kasancewa ba don 'yan siyasar ƙasar sun fi mayar da hankali kan abin da zai amfane su ba - maimakon abin da zai amfani ƙasar.

Amma akwai munanan abubuwa da suka auku.

Destroyed property in Lekki suburb in Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa ta sata da wawaso a Legas a ranakun Laraba da Alhamis

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fasa shaguna, kuma sun wawashe manyan ɗakunan ajiyar kaya har ma da kamfanonin fitattun ƴan siyasa.

Duk da manufar wadannan gungun matasan biyu sun sha bamban, amma suna da abin da ya haɗa su: shi ne ganin mutuncin masu mulki.

Sai dai zai yi wuya tafiyarsu ta zama ɗaya. Duk wani yunkuri na hada su wuri guda ba zai yiwuba, saboda wasunsu ba za su amince su yi tafiya da waɗanda ake kallo da "muggan halaye".

Bayanan bidiyo, Bidiyo: 'Bala'in da muka gani a zuwan sojoji wajen zanga-zangar EndSars'

'Buhari bai san inda aka nufa ba'

Duk da haka akwai alamar masu mulki sun gane cewa talauci da wahalar rayuwa sun zama abubuwan da ke barazana ga tsaron ƙasa, kamar yadda Mista Kakanda yake kallon lamarin.

"Gwamnati ta gane cewa ba za ta iya ci gaba da kau da kai ga fusatar matasa kamar yadda ta saba yi a da ba," inji shi.

Sai dai ta yi tuntuɓi ba sau ɗaya ba yayin da ta ke ƙoƙarin kashe wutar boren.

Shugaba Muhammadu bUhari ya yi wa ƙasar jawabi ranar Alhamis da daddare, "kuma yawanci bai san inda aka nufa ba", inji Japeth Omojuwa, wani marubuci kan al'amuran yau da kullum a intanet.

Shugaba Buhari ya bukaci a kawo ƙarshen zanga-zangar kana a fara tattaunawa, amma "tarihi zai tuna da shi a matsayin wanda yayi wa ƴan Najeriya barazana saboda kawai sun buƙaci gwamnatinsu ta amince za ta yi adalci."

End Sars protesters

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu nazari na ganin kamata yayi masu zanga-zangar su mayar da hankali kan sauye-sauyen da suke buƙatar a yi wa ƴan sanda

Duk da haka Mista Omojuwa yayi amanna cewa gwagwarmayar ta #EndSARS za ta iya cimma wani abu.

Kada ta yi dogon buri na samun iko irin na siyasa, inji shi, amma kamata yayi su tabbatar masu mulki sun cika alƙawuran da ska ɗauka na sauye-sauye da yi wa ƴan sanda masu laifi shari'a.

Irin waɗannan ƙananan matakan ne za su iya kawo gagarumin sauyi.