Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EndSARS: An saka dokar hana fita a Jihar Edo sakamakon tarzoma
Gwamnatin Jihar Edo ta saka dokar hana fita tsawon awa 24 biyo bayan harin da aka kai wa 'yan sanda da kuma kuɓutar da fursunoni daga gidan yari a Benin, babban birnin jihar.
Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Edo Osarodion Ogie ya fitar, ta ce dokar hana fitar "za ta ci gaba da kasancewa har baba ta gani".
Ogie ya ce 'yan daba sun ƙwace iko da zanga-zangar #EndSARS kuma gwamnati "ba za ta zira ido ba yayin da ake kai hare-hare".
"Dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe 4:00 na yammacin 19 ga watan Oktoban 2020," in ji sanarwar.
"Wannan matakin ya zama dole saboda abubuwan da ke faruwa na ɓarna da hare-hare a kan mutane da ma'aikatu da sunan zanga-zangar #EndSARS."
Rundunar 'yan sandan a jihar ta ce an kai wa ofisoshinta guda uku hari tare da yin awon gaba da makamai a birnin Benin na Jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna fursunoni na tsallake katanga daga wani gidan yari.
Kazalika, maharan sun saki wasu da ake tsare da su a ofisoshin kafin daga bisani su cinna musu wuta, a cewar 'yan sanda.
"Yayin da gwamnatin Edo take mutunta haƙƙin 'yan ƙasa na yin zanga-zangar lumana, ba za ta ƙyale 'yan daba su riƙa ɗaukar doka a hannunsu ba domin cuzguna wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da kuma jihar baki ɗaya.
"Bisa wannan umarni, makarantu da wuraren kasuwanci za su kasance a rufe."
Ofisoshin da aka kai harin sun haɗa da Ugbekun Police Station da Oba Market Police Station da Idogbo Police Post, in ji rundunar, wanda aka kai a yau Litinin, 19 ga watan Oktoban 2020.
"Rundunar na yin bakin ƙoƙarinta zuwa yanzu domin shawo kan lamarin da kuma kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa," a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.