SARS: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga kan #EndSars a Abuja

Asalin hoton, TWITTER/SASSY_AYOM_/via REUTERS
'Yan sandan Najeriya sun harba hayaƙi mai sa ƙwalla kan masu zanga-zangar da ke son a soke rundunar SARS da ke yaƙi da 'yan fashi da makami a Abuja babban birnin ƙasar.
Suna zanga-zangar ce bayan wani bidiyo ya karaɗe shafukan intanet inda ya nuna yadda wasu da ake zargi jami'an SARS ne sun kashe wani mutum.
An gudanar da jerin irin wannan zanga-zanga a birane da dama na ƙasar, ciki har da Lagos. Taurarin fina-finai irin su John Boyega da Mr Macaroni na cikin waɗanda suka halarci zanga-zangar.
Tun da farko masu zanga-zangar sun nuna matuƙar rashin jin daɗinsu kan jami'an rundunar Special Anti-Robbery Squad (Sars), wadda ake zargi da azabtar da mutane da kisan kai.
'Yan ƙasar suna amfani da maudu'in #EndSARS a dandalin Twitter bayan fitowar bidiyon da ake zargi jami'an rundunar SARS sun kashe wani matashi ranar Asabar da ta wuce.
Mutane da dama kuma suna amfani da maudu'in domin jan hankali kan musgunawar da 'yan sandan ƙasar suke yi musu.
Ranar Lahadi babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya haramta wa rundunar ta Sars tsare mutane a shingayen duba ababen hawa da kuma sanya shingayen.
Ya kuma ce dole jami'an Sars su riƙa sanya kayan aikinsu wato uniforms sannan ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan abin da ya faru
Sai dai masu zanga-zangar sun nace cewa dole a soke rundunar baki ɗaya kowa ya huta.
An ji ƙarar harbin bindiga
Ranar Juma'a masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa hedikwatar rundunar 'yan sandan da ke Abuja.
Wani da ya halarci zanga-zangar, Brian Dennis, ya shaida wa BBC 'yan sanda sun riƙa harba hayaƙi mai sa ƙwalla kuma sun doki wasu daga cikinsu.
Hotunan bibiyon da aka wallafa a Twitter sun nuna yadda masu zanga-zangar ke guje wa hayaƙi mai sa ƙwalla da aka harba musu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wata mace da ta halarci zanga-zangar Anita Izato ta ce ta ji ƙarar harbin bindiga kuma daga nan ne suka gudu domin tsira da rayuwarsu.
Yau ce rana ta biyu da ake zanga-zangar a birnin Lagos, inda madsu zanga-zangar suka kwana a wajen gidan gwamnatin Lagos.
Ana jan ƙafa wajen yin sauyi
Maudu'in #EndSARS ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi tattaunawa a Twitter a duk faɗin duniya ranar Juma'a inda fitattun mawaƙa da 'yan wasan kwaikwayo irin su Wizkid da Davido suka goyi bayan masu zanga-zangar.
Tauraron fim ɗin The Star Wars John Boyega, wanda ɗan asalin Najeriya ne, ya wallafa saƙon Twitter inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ba a samun sauyi a aikin ɗan sandan ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
An soma amfani da maudu'in #EndSARS tun 2018.
A watan Mayun 2019 hukumar kare hakkin ɗan adam ta Najeriya ta wallafa wani rahoto kan abubuwan ta'asar da Sars ke yi sai dai mutane sun ce an gaza samun sauyi kan hakan.
Wani bincike da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta wallafa a watan Yuni ya zargi jami'an rundunar Sars da "azabtarwa da kuma yin amfani da wasu hanyoyin da ba su dace ba wurin ƙwaƙulo bayanai daga wurin mutanen da ake zargi da aikata laifuka".
Ta wallafa ƙorafe-ƙorafe 82 da ta ce an kai mata a kan Sars tsakanin watan Janairun 2017 zuwa watan Mayu na 2020.
Amnesty ta gano cewa jam'an Sars sun fi mugunawa maza masu tsakanin shekara 17 zuwa 30.











