Yadda mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya a Kano suke ibadunsu

Babu takamaiman adadin mabiya ɗarikar Ƙadiriyya a Najeriya, amma ana ƙiyasin cewa sun kai miliyoyi.

Ɗarikar ta Ƙadiriyya na daga manyan ɗarikun sufaye da ake bi a Najeriya, kuma ana ɗaukanta a matsayin ɗarikar da ta fi daɗewa a ƙasar.

Sidi Abdulkadir Jilani ya rayu ne a birnin Bagadaza na kasar Iraki tsakanin shekarun 1078 zuwa 1166. Yana daga manyan waliyyai da mabiya ɗarikun Sufaye suke girmamawa, har ma ana masa kirari da sarkin waliyyyai.

Matan da ke alfahari wajen iya ƙira'ar Ƙur'ani

Bidiyon yadda ake satar gari a wajen niƙa a Kano

Nahiyar Afirka na daga yankunan duniya da ke da mabiya ɗarikar ta Ƙadiriyya da dama, kuma a yanzu birnin Kano a Najeriya ne cibiyar ɗarikar ta Afirka, kasancewar shugabanta Shaikh Karibullah Nasiru Kabara yana zaune ne a Kano.

Shiekh Karibu ya gaji shugabancin ɗarikar ne daga wajen mahaifinsa Shaikh Nasiru Kabara shekara 25 da ta gabata.

Gabanin zama shugaban ɗarikar na nahiyar Afirka baki daya, marigayi Sheikh Nasiru Kabara ya zama shugaban ɗarikar na nahiyar Afirka ta yamma. Ya rasu a watan Oktoban 1996.

Yaushe darikar Kadiriyya ta shiga Najeriya?

Babu bayanai na ainihin shekarar da ɗarikar ta shiga kasar. Sai dai wasu bayanai na cewa an fara bin ɗarikar ta Ƙadiriyya a Najeriya ne tun zamanin Sidi Abdulkadir Jilani, wanda ya kafa ɗarikar, fiye da shekaru 900 da suka wuce.

Ɗaya daga malaman ɗarikar, Sheikh Jamilu Alkadiri ya bayyana cewa "Ɗarikar Ƙadiriyya ta shigo Najeriya tun da rayuwar Sidi Abdulkadir din da kan shi RA".

"Sannan babu Najeriyar sai dai a ce Biladus-Sudan."

Ya kara da cewa ɗaya daga manayn malaman da aka yi a Najeriya, Waziri Junaidu ya tabbatar da haka. "Har da akwai wasu wurare da ake nunawa a Ƙauran Namoda (a jihar Zamfara) da ake cewa shi kansa Sidi Abdulkadir ya zo nan," a cewar Alkadiri.

Ya ce mutane suna zuwa ziyara.

Bayanai kuma sun tabbatar da cewa Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo wanda ya jaddada Musulunci a Najeriya ya yi ɗarikar ta Ƙadiriyya.

Mabiya ɗarikar suna gudanar da wasu al'amura na ibada da suka bambamta su da sauran mabiya ɗarikun sufaye.

Daga cikin akwai Zikirin Anfasu da ake yi da numfashi, wanda Sheikh Karibullah ya ce daya ne daga cikin nau'ikan zikirai da ake yi da dukkan gabbai.

Sannan akwai buga bandiri ko mandiri wanda ake yin zikiri da shi, musamman ambaton Allah da yabon Manzon Allah SAW da kuma waliyyai, kamar Sidi Abdulƙadiri.

Sai dai wasu Musulmin na ganin mabiya ɗarikar sun saba koyarwar addinin Musulunci wajen gudanar da ibadun, to amma mabiya Ƙadiriyyar na cewa rashin fahimta ne ya sa ake sukar su, domin suna da hujjoji kan duk abin da suke yi.