'Ƴan ci ranin Habasha na mutuwa a cibiyoyin da aka tsare su a Saudiyya - Amnesty

Ethiopian migrants are seen inside a building while undergoing quarantine as they across Yemen's land to reach Saudi Arabia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Waɗanda ake tsare da su ɗin an kore su ne daga ƙasar Yemen da ke maƙwabtaka

A ƙalla mutum uku ne suka mutu a cibiyoyin da ake tsare da dubban ƴan ci ranin Habasha a Saudiyya, kamar yadda ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta ce.

Ƴan ci ranin na fuskantar ''azabtarwa mara misali'' - da suka haɗa da ɗaure mutum biyu da sasari ɗaya, sannan suke yin duk najasarsu a inda suke zaune, a cewar ƙungiyar.

Amnesty ta kuma nemi hukumomin Saudiyya da su inganta yanayin da cibiyoyin ke ciki.

Waɗanda ake tsare da su ɗin an kore su ne daga ƙasar Yemen da ke maƙwabtaka.

Ƴan ci rani daga Habasha da sauran ƙasashe sun daɗe suna aiki a arewacin Yemen, amma ƴan tawayen Houthi suka tilasta musu barin wajen, in ji Amnesty.

A cewar hukumar Kula da Ƙaurar Mutane Ta Duniya IOM, akwai ƴan Habasha 2,000 da suka maƙale a kan iyakar Yemen, ba tare da samun abinci ko ruwa ko kula da lafiyarsu ba.

Dubban ƴan Habasha na zuwa Saudiyya don yin aiki, al'amarin da ya sa ƙasar ta zama wata jarin samun kuɗin shiga ga Habasha.

Saudiyya tana ta ƙoƙarin hana ƴan ci rani shiga ƙasar ba bisa ƙai'da ba.

Akwai kusan ƴan ci ranin Habasha da suke zaune a Saudiyya ba bisa ƙa'ida ba har 500,000 a lokacin da ƙasar ta fara aikin mayar da su ƙasashensu a 2017, a cewar IOM.

A ƙalla ƴan Habasha 10,000 ake mayar wa gida kowane wata, amma a farkon shekarar nan jami'an Habasha sun nemi a dakatar da hakan saboda annobar cutar korona, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

A watannin baya-bayan nan, Habasha ta yi ta fafutukar samar da isasshen wajen da za ta killace mutanen da ake mayarwa tare da tabbatar da cewa ba su koma ƙasar ɗauke da cutar korona ba.

Gawarwaki

Amnesty ta yi hira da wasu mutum 12 ƴan Habasha da aka tsare kan yanayin da suke ciki a cibiyar tsare mutane ta al-Dayer, da gidan yarin Jizan da wasu gidajen yari a Jiddah da Makkah.

Ana cikin yanayi marar kyau musamman a cibiyar al-Dayer da Jizan, inda waɗanda ake tsare da su suke ce mutum 350 ne a cikin ɗaki ɗaya, in ji Amnesty.

Map

Ƙungiyar ta ce wasu ƴan ci rani biyu sun bayar da rahoton cewa sun ga gawar mutum uku da idonsu - wadanda suka fito daga Habasha da Yemen da Somaliya - a cibiyar al-Dayer.

''Haka kuma, dukkan waɗanda aka yi hira da su sun ce sun san mutanen da suka mutu a tsare, sannan mutum huɗu sun ce sun ga gawarwaki da idonsu,'' in ji rahoton.

Amnesty ta ce hotuna da bidiyo da hotunan tauraron ɗan adam sun tabbatar da zarge-zargen.

Ta kuma nemi gwamnatin Habasha da ta yi gaggawar tsara mayar da ƴan ƙasarta, a yayin da ta nemi hukumomin Saudiyya da su inganta yanayin cibiyoyin tsare mutanen a halin yanzu.

Habasha ta shirya mayar da ƴan ci ranin da ake tsare da su 2,000 nan da tsakiyar watan Oktoba, kamar yadda Tsion Teklu, ƙaramar ministar harkokin wajen Habasha ta shaida wa AFP a watan da ya gabata.

Ta ce yawan ƴan ci ranin Habasha da ke cibiyoyin tsarewa 16,000 ne a farkon shekarar nan, amma tuni yawan ya ragu.

A watan da ya gabata ƴan ci rani uku ne suka shaida wa AFP cewa wasu jami'an diflomasiyyar ƙasarsu da suka kai ziyara sun gargaɗe su da su daina magana a kan yanayin da cibiyoyin da ake tsare da su ɗin ke ciki.