Hukumomin Saudiyya sun mayar da 'yan ciranin Habasha gida

Wasu 'yan ciranin Habasha da ake kokarin mayarwa gida

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu 'yan ciranin Habasha da ake kokarin mayarwa gida

Kusan mata da yara 'yan Habasha dari da hamsin ne aka mayar da su gida daga Saudiyya bayan shafe tsawon lokaci suna kokawa a kan ci gaba da tsare su a wasu cibiyoyin daurarru.

A farkon wannan shekarar ne hukumomin Saudiyya suka fara tasa keyar dubban 'yan Habasha da ba su da takardu da suka je can neman aiki.

Lokacin da ta isa babban birnin kasar Addis Ababa, wata mata ta shaida wa BBC cewa ta kwashe watanni shida a wani sansanin da ake tsare da ita, tana barci a kasa.

Ta ce mutanen da suka yi rashin lafiya ba su sami taimakon likita ba.

Gwamnatin Habasha ta sha suka kan yadda ta yi jinkiri wajen taimakawa bakin hauren da suka makale.

Sai dai hukumomin kasar sun dora alhakin hakan a kan cutar korona, wadda suka ce ta janyo karancin wuraren kebe mutane.

Halin da 'yan gudun hijira ke ciki a duniya

majalisar dinkin duniya ta ce 'yan cirani na cikin mawuyacin hali a duniya
Bayanan hoto, majalisar dinkin duniya ta ce 'yan cirani na cikin mawuyacin hali a duniya

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da 'yan gudun hijira ta fitar da wani rahoto inda ta bayyana cewa cikin yara 'yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari bakwai na duniya, rabinsu ba su samun ilimin boko.

Ta bayar da dalilai da suka hada da bukatar bayar da muhimmanci ga kare lafiyar yara sama da ba su ilimi, da kuma gazawar da iyayen yara ke yi na kasa biyan kudin makaranta.

Hukumar ta ce damar da yara 'yan gudun hijira ke da ita na samun ilimin sakandare na dada raguwa yayin da suke kara girma.

Hukumar ta yi kira ga gwamnatoci da kuma makarantu da kamfanoni masu zaman kansu da su zuba jari wajen fito da kyakkyawan shirin da zai tabbatar yaran sun samu rayuwa mai inganci.