Hachalu Hundessa: 'Abokina, mawaƙin da kisansa ya jawo tarzoma a Ethiopia'


Kisan da aka yi wa mawaƙin nan ɗan asalin Ethiopia, Hachalu Hundessa, ya sa an shafe kwanaki da dama ana tarzoma a ƙasar, inda a ƙalla mutum 80 suka mutu.
Hachalu ya shafe galibin rayuwarsa yana waƙa kan batun soyayya da haɗin kai, amma duk da haka waƙoƙinsa na jan hankali kan nuna wariya da ake yi wa ƙabilarsa ta Oromo.
Wani mai sarrafa kyamara a BBC mai suna Amensisa Ifa, wanda aboki ne ga mawaƙin kafin mutuwarsa kuma wanda ya naɗi wani bidiyon waƙarsa da ta samu lambar yabo, ya yi waiwaye kan abubuwan da suka faru tun bayan mutuwarsa.
Wani lokaci idan na tuna da batun mutuwar Hachalu, sai na yi tunani ina ma ni na mutu domin shi ya rayu.
Ya kasance wani gwarzo ga mutane da dama, kuma yana da abubuwa da dama da zai ba mutane.
Ya yi wa jama'a yaƙi - a lokutan da mawaƙa da 'yan siyasa suka gudu suka bar ƙasar, Hachalu ya tsaya tsayin-daka ya bujuro da batutuwa da mutane da dama ba su isa su tattauna a kansu ba.

'Hachalu yana asibiti'
Na fara samun kiran waya da sakonni wurin ƙarfe 10:00 na dare a ranar Litinin daga abokaina waɗanda sai tambaya ta suke yi me ya faru da Hachalu.
A lokacin babu wanda yake cewa Hachalu ya mutu, amma da alamu wani abu ya faru da shi.
Na yi ƙoƙarin kiran sauran abokaina, amma babu wanda ya amsa kiran. Sai na samu wani saƙo da ke cewa Hachalu na asibiti.
Na yi ƙoƙarin tuƙa mota na tafi can, a kan hanya ta, na yi ƙoƙarin tuntuɓar wani daga cikin abokanmu ta waya, sai ya faɗa mini cikin karkarwa cewa yana tsaye kusa da gawar Hachalu.
An harbe Hachalu.

Ko da na isa asibitin, ana ta koke-koke a cikin daƙin da gawar take.
Wani sai ya cire lulluɓin gawar sai na ga wani abu mai kama da harbin bindiga a ƙirjinsa.
Akwai 'yan sanda a wurin, da kuma abokansa da dama.
Ina kiran sunansa ina kuka, kowa na ihu, kowa na kuka.
"Kad dai ku ce da gaske ya mutu," sai muka ci gaba da ihu.

Sai aka tafi da gawar Hachalu zuwa wani asibiti domin likitoci su yi bincike, inda muka bi motar ɗaukar gawar.
Mun tsaya tsawon daren. Da misalin ƙarfe 04:00, sai muka fita waje inda muka ga mutane sun cika maƙil sakamakon samun labarin mutuwar Hachalu.
Kowa na kuka yana kiran sunansa.
Sai bayan da rana ta fito muka yi ƙoƙarin fitar da gawar zuwa wajen babban birnin ƙasar wato Addis Ababa zuwa mahaifar Hachalu wato Ambo - kimanin kilomita 100 daga babban birnin.
"Hachalu gwarzonmu ne"
A daidai lokacin da muka fita daga babban birnin cikin ayarin motoci, sai na ga cewa ana rikici, ina jin ƙarar harbin bindiga inda kuma 'yan sanda na ta harba hayaƙi mai sa hawaye.
Muna ta tafiya har muka isa garin Burayu, kusan kilomita 15, a nan ma mun tarar da dubban mutane waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa Addis Ababa a ƙafa, wasu a cikin motoci, akasarinsu na cikin ɗimuwa inda kuma suke so su yi bankwana ga Hachalu.
Waɗannan mutane ne daga sassa daban-daban na Oramio wadanda suka niƙi gari tun cikin dare bayan jin labarin mutuwarsa. Da dama na ta roƙon a gudanar da jana'izarsa a babban birnin ƙasar.
Ina zaune a motata, sai na ji mutane na cewa: "Hanchalu gwarzon mu ne. Ya cancanci ya samu jana'iza irin ta gwaraza a Addis."

Sai ayarin motocinmu suka tsaya a wurin na ɗan wani lokaci, sai muka sake tafiya domin komawa Addis Ababa.
Sai daga baya muka gano cewa gwamnati ta kafe kan cewa sai dai a binne Hachalu a Ambo, sabon abin da iyalansa ke so kenan. Wannan ne ya sa aka saka gawarsa cikin jirgi mai saukar ungulu zuwa mahaifarsa.
Amma na kasa zuwa Ambo wurin jana'izarsa a ranar Alhamis sakamakon toshe hanyoyin zuwa garin.

Asalin hoton, Reuters
Hakan ya sa na kalli jana'izar tasa a talabajin, wannan ya kasance lokaci mai ƙunci a gare ni.
Na so a ce ina tare da shi domin na yi masa sallama yadda ya dace. Na ga cewa ba a bar mutane da yawa sun halarci jana'izar ba, kuma a al'adarmu, ba za a iya birne mutum da mutane kaɗan ba, ballantana gwarzo kamar Hachalu.
A daidai lokacin da nake kallo, sai kuka nake yi.
Sai na kira mahaifiyata cikin hawaye na shaida mata cewa: "Ina so na mutu a yau kuma tun lokacin nake kuka, duk lokacin da wani ya tambaye ni ya nake ji.

Asalin hoton, Reuters
Har yanzu ina cikin ɗimuwa kan batun mutuwar Hachalu.
Ko a ranar Alhamis, bayan na samu labarin cewa wani abu ya faru da wani abokinsa, nan take na fara kiran lambar Hachalu domin na yi masa magana a kai.
Na yi magana da shi mako guda kafin a harbe shi sai ya faɗi mini cewa ya yi wata sabuwar waƙa da zai saka mini mai suna "Eessa Jirta?" mai nufin kana ina?
Waƙoƙin Hachalu ba sun tsaya a siyasa ba ne kaɗai, ya yi waƙa kan al'adu da haɗin kai da haƙƙin ɗan adam da soyayya da dai sauransu.
Na so na yi magana da shi kan wata tattaunawa da ya yi inda ya bayyana cewa ba zai juya bayansa kan batun siyasa ba.

Asalin hoton, Dagi Pictures
Yana magana ne kan batun haƙƙin mutanen Oromo, waɗanda su ne ƙabila ma fi girma a duk Ethiopia waɗanda sun daɗe suna kokawa kan batun nuna wariya da ake yi musu ta ɓangaren siyasa da tattalin arziƙi.
Mutane da dama na zarginsa da ƙarɓar kuɗi daga sabuwar jam'iyyar da ke mulkin ƙasar - sai dai ya musanta wannan zargi, inda ya ce: "Babu wanda zai iya saye na."
Ya san cewa yana da maƙiya, kuma ya sha samun matsala da mutane a Addis Ababa.
Amma bai taɓa damuwa kan rayuwarsa ba. Ya sha cewa duk wanda ya mutu saboda mutanensa, gwarzo ne.
"Ba ni da bambanci da kowa," haka ya taɓa faɗa mini, " Zan iya mutuwa wata rana, amma ba na tsoron mutuwa."











