Masar da Habasha sun cimma yarjejeniya kan Kogin Nilu

Madatsar ruwar da Habasha za ta gina tashar lantarki
Bayanan hoto, Madatsar ruwar da Habasha za ta gina tashar lantarki

Kasashen Habasha da Masar sun cimma yarjejeniyar kan gina babbar madatsar ruwa da Habasha ke yi a Kogin Nilu.

Kasashen sun cimman yarjejeniyan kan muhimman batutuwan da suka shafi gina madatsar inda a nan Habasha ke gina tashar wutar lantarki mafi girma a nahiyar Afirka.

An dade ana fargabar batun gina tashar lantarkin wadda ake sa ran za ta fara aiki a cikin wannan shekarar, na iya haddasa yaki.

Hakan ya biyo bayan damuwar da Masar da Sudan suka nuna cewa tsasar za ta rage yawan ruwan da da suke samu daga kogin na Nilu.

Bayanan tattaunawar da suka fara fitowa na cewa yanzu Habasha da Masar sun samu daidaito kan yadda za a cika tashar da ruwan Kogin.

A baya masar ta nemi a tara ruwan da tashar za ta yi amfani da shi a hankali cikin shekaru saboda kar hakan ya rage ruwan da ke shigowa kasarta wadda tattalin arzikinta ya dogara a kan albarkatun ruwa.

Ana sa ran kasashen za su rattaba hannu a kan yarjejeniyar a cikin watan Fabrairun nan da muke ciki.