Ana fargabar barkewar rikici kan kogin Nilu

Shugaba Abdel Fatta al-Sisi na Masar, Omar Al-Bashir na Sudan da Firai Ministan Habasha Heilemariam Desalegn

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Shugabannin kasashen Masar da Habasha da Sudan sun tattauna kan batun madatsar ruwa ta Nilu a watan Junairun 2018

Wani kogi ya ratso ta tsakanin kasashen Afurka 11 da suka hadar da Masar, da Habasha da kuma Sudan, wadanda ke cikin rikici kan gina madatsar ruwa a kan hanyar da ruwan kogin ke bi.

Wannan shi ne kogi mafi tsawo a duniya da ke tsakiyar wani waje mai cike da siyasa, da ake tsoron barkewar yaki tsakanin kashen da suke amfani da ruwansa.

Kasar Masar ta dogara ne kacokam ga wannan kogi domin kuwa ta nan take samun ruwanta, ta na cike da fargabar mutanenta za su iya shiga wani hali da zarar an kammala ginin madatsar ruwan da za ta lakume dalar amurka biliyan hudu, kafin kammala ta a karshen shekarar nan.

A nata bangaren kasar Habasha na cewa, tana da dukkan 'yancin da za ta iya datsar ruwan daga kogin Nilu kuma tana daukar hakan a matsayin abin da zai bunkasa tattalin arzikinta.

An yi zaman tattaunawa har karo hudu amma an gaza cimma matsaya, inda bangarorin biyu ke bigewa da zargin juna. Sileshi Bekele shi ne Ministan ruwa na Habasha.

Rigimar akan adadin ruwan da za a saki ya gangaro kasashe irinsu Masar ne, wadda ke son Habasha ta ba ta tabbacin ba za ta hana kogin gangarowa ba musamman a lokacin fari.

Duk da gaza cimma matsaya kan tattaunawar da aka yi a baya bayan nan, Shugaban Masar Abdulfatah Al Sisi ya ce yana da kwarin gwiwar za a samu matsaya a cikin makon nan, kuma ba ya tsoron barkewar wani yaki tsakaninsu da Habasha.

Amurka da Bankin duniya sun taka rawar gani wajen dawo da kasashen kan teburin sulhu lokacin da aka kasa cimma yarjejeniya. Wakilan duka kasahe ukun sun tattauan da shugaban Amurka Donald Trump wanda gwamnatinsa ke da yakinin za a cimma yarjejeniyar. Dakta Hassan Khamenji wani mai sharhi ne kan kasashen gabashin Afrika.

Wannan tattaunawar a Washington na da mahimmanci ba wai kawai rikicin kasashen ba, ko shakka babu zai sauya yadda kasashen za su rika amfani da ruwan dake fitowa daga kogin Nilun.