Yadda Masar ta kusan hana aikin jarida a kasar

Mada Masr is Egypt's last major independent media outlet (file photo)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mada Masr ce jarida ta karshe ta intanet mai zaman kanta a Masar
Lokacin karatu: Minti 2

Wata jarida ta intanet mai zaman kanta a Masar ta ce jami'an 'yan sanda sun kai wani samame a ofishinta da ke al-Kahira.

Jaridar mai suna Mada Masr ta wallafa wani sakon gaggawa a Facebook wanda ke cewa jami'an tsaron kasar sun kutsa cikin ofishinta babu izini.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Wannan samamen na zuwa ne kwana guda bayan da jaridar ta sanar da cewa 'yan sanda sun kama wani editanta tare da wasu 'yan jarida da ke ma ta aiki.

Daga baya hukumomi sun sako 'yan jaridar, amma ba a mayar ma su da wayoyinsu na hannu da komfutocinsu ba.

An sako ma'aikatan jarida ta karshe mai zaman kanta a Masar bayan da jami'an 'yan sanda na farin kaya suka kai wani samame ofishinsu da ke birnin al Kahira.

An kuma sako wani dan jaridar Shady Zalat wanda aka kama ranar Asabar.

Sharif Abdel Khoudous ma'aikacin jaridar ne, kuma ya bayyana wa BBC yadda samamen ya auku:

"Sai dai mu yi hasashen dalilan da suka kawo su nan, domin sun ki amsa tambayoyin da muka yi musu, kai sun ma ki bayyana ko su wa ye."

Ya kuma ce a watannin baya, Mada Masr ta sha matsi daga hukumar kasar nan saboda ayyukanta na kare 'yancin aikin jarida.

Wani allo da hoto shugaban Masar al Sisi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani allo da hoto shugaban Masar al Sisi a birnin al Kahira

Jami'an tsaro sun yi awon gaba da wani editan jaridar ta Mada Masr mai suna Shady Zalat tun da sanyin safiyar Asabar daga gidansa, kuma an shafe kusan yinin babu wanda ya san inda ya ke.

"Muna kallon wannan matakin a matsayin wanda ka iya kawo karshen ayyukan jaridar baki daya", inji Sharif.

Ya ce za su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da hatsarin da 'yan jarida ke fuskanta a Masar.

"Akwai hatsarin yin aiki a jaridar Mada Masr. Ina nufin an dode shafinmu na intanet tun watan Mayun 2017 a Misra."

Ya kara da cewa, "mun gano cewa an shafe shekaru ana takura wa 'yan jaridu har ta kai ga ana rufe wasunsu, wasu kuma an tilasta mu su mika wuya ga masu mulki."

Jaridar Mada Masr ta kasance kusan ta karshe irinta mai zaman kanta da ke iya sukar lamirin gwamnati da kawo yanzu ta ci gaba da aiki a kasar.

A 'yan shekarun nan - musamman a karkashin mulkin Shugaba al Sisi - hukumomin kasar sun matsa wa kafofin yada labarai da ke sukar ayyuka da matakan gwamnatin da suka saba wa adalci da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.