Ana kamen masu zanga-zanga a Masar

Alaa Abdel Fattah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alaa Abdel Fattah

Rahotanni daga Masar na cewa an kama wani fitaccen mai adawa da gwamnatin kasar wata shida bayan da aka sako shi daga kurkuku.

Iyalan gidan Alaa Abdel Fattah, ne suka bayyana haka. Abdel Fattah, wanda a watan Maris aka sako shi bayan ya shafe shekara biyar a tsare saboda ya shirya wata zanga-zanga babu izini.

Yana cikin wadanda suka yi fice wajen boren da aka yi wa tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak a 2011.

A karkashin hukuncin da aka gindaya masa, tilas ne ya rika kwana a ofishin 'yan sanda har na tsawon shekara biyar.

Iyalansa sun ce a ranar Lahadi aka sake kama shi, a daidai lokacin da yake shirin ficewa daga ofishin 'yan sanda.

Wata 'yar uwarsa mai suna Mona ta sanar da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Da na isa ofishin 'yan sandan, sai na taras da babu kowa a wurin da yake kwana."

Rahotanni sun ce an sake kama shi ne saboda ya wallafa labaran kanzon kurege da niyyar tunzura mutane domin su yi wa gwamnati bore.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce kimanin mutum 2,000 aka kama tun da aka fara wani sabon bore a birnin al-Kahira da wasu biranen kasar a makon jiya.