Ƴan majalisar dokokin Malawi sun ƙi karɓar gudunmowar kwaroron roba 200,000

Asalin hoton, Malawi Parliament
Ƴan majalisar dokokin Malawi sun ƙi karɓar gudunmowar fiye da kwaroron roba 200,000 daga gidauniyar agaji ta Aids Health Foundation.
An bayar da kwaroron robar ne don a ajiye su a banɗakunan da ke cikin ginin majalisar.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Richard Chimwendo, ya ce mambobin majalisar ba sa buƙatar irin wannan taimakon don kuwa za su iya sayen kwaroron robar da kuɗinsu.
An bayar da gudunmowar ce ta hannun shugabar kwamitin lafiyar jiki Maggie Chinsinga.
Mista Chimwendo ya ce wani rahoto da wata jaridar ƙasar ta wallafa kan gudunmowar - cin mutunci ne ga ƴan majalisar.
Rahoton ya ambato Ms Chinsinga tana cewa majalisar dokokin tana bayar da kusan kwaroron roba 10,000 a kowane wata, kuma a wasu lokutan ''har sukan ƙare mata,'' kamar yadda jaridar gwamnatin Malawi ta ruwaito.
Mataimakin kakakin majalisar, Madaliotso Kazombo, ya ce hakan ba gaskiya ba ne kuma ya nemi jaridar ta bayar da haƙuri.







