An yi kiranyen kwaroron roba a Uganda

Wata kungiya mai suna Marie Stopes ta ce sun yi wa kwaroron roba da abokan huldarsu suka saya a kasar Uganda kiranye saboda rashin kyawunta.
Gwaje-gwajen da aka yi wa kwaroron robar Life Guard da wani kamfanin kasar India ke samarwa sun nuna sun lalace, inda suka samu kananan huda a jiki, kamar yadda hukumar binciken ingancin abinci da magunguna ta Uganda ta sanar.
Kamfanin Marie Stopes ya yi fice wajen samarwa kasashe sama da 35 maganin tsarin iyali.
Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kusan kashi shida na matasan Uganda na dauke da kwayar cutar HIV.
Ko Uganda za ta iya magance yaduwar cutar HIV?
Batun yi wa maza Shayi ka iya rage yaduwar cutar HIV a kasar Uganda.
A kowanne wata kamfanin Marie Stopes na kai katan din kwaroron roba miliyan daya da dubu dari biyar kasar Uganda.
A sanarwar da kamfanin ya fitar wadda BBC ta gani, ta tabbatar da wannan ne karon farko da aka samu akasi kan kwaroron robar dan haka ne ma sukai saurin yin kiranyen.
Wannan na zuwa ne bayan gwajin da hukumar ingancin abinci da magunguna ta Uganda ta yi kan kwaroron robar, inda ta shaida wa kamfanin Marie Stopes cewa Life Guard da aka kai kasar a ranar 30 ga watan Nuwamba ba ta da inganci.











