Zaben Edo: INEC ta ce Gwamna Obaseki na PDP ya doke Ize-Iyamu na APC

Asalin hoton, Twitter/Obaseki
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Wannan ne karo na biyu da Obaseki ke doke Ize-Iyamu, inda a 2016 ma hakan ya faru, amma lokacin Obaseki na APC, Ize-Iyamu kuma a PDP.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu ƙuri'u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri'u 223,619.
Ɗan takarar Jam'iyyar SDP ne ya zo na uku da ƙuri'u 323, sai kuma na Jam'iyyar LP da ya samu ƙuri'u 267.
Hukumar ta ce adadin waɗanda aka tantance domin kaɗa ƙuri'a 557,443, adadin ƙuri'u masu sahihanci 537,407.
Adadin ƙuri'un da aka jefa 550,242 sai kuma ƙuri'un da suka lalace a zaɓen 12,835.
'Yan takara 14 ne suka kara a zaɓen wanda ya gudana a ranar Asabar, 19 ga watan Satumbar 2020.
Jihar na da rumfunan zaɓe 3,035 sannan akwai sama da mutum miliyan biyu da aka yi wa rajistar zaɓen, sai dai waɗanda suka jefa ƙuri'ar ba su wuce dubu 600 ba.
Zaɓen Edo dai kamar yadda masana siyasa suka bayyana, tamkar wani zakaran gwajin dafi ne tsakanin APC da PDP da ma ita kanta hukumar INEC.
Yadda aka yi karon batta tsakanin PDP da APC a ƙananan hukumomi 18 na Edo
Karamar Hukumar EGOR
APC: 10202
PDP: 27621
Karamar Hukumar OWAN EAST
APC: 19295
PDP:14762
Karamar Hukumar OVIA NORTH EAST
APC: 9,907
PDP: 16,987
Karamar Hukumar ETSAKO WEST
APC: 26,140
PDP: 17,959
Karamar Hukumar ESAN WEST
APC: 7,189
PDP: 17,434
Ƙaramar Hukumar ESAN SOUTH EAST
APC: 9237
PDP: 10563
Ƙaramar Hukumar OREDO
APC: 1836
PDP: 43498
Ƙaramar Hukumar IKPOBA OKHA
APC: 18218
PDP: 41030
Ƙaramar Hukumar IGUEBEN
APC: 5199
PDP: 7870
Ƙaramar Hukumar OWAN WEST
APC: 11193
PDP: 11485
Ƙaramar Hukumar ESAN CENTRAL
APC: 6719
PDP: 10794
Ƙaramar Hukumar ESAN NORTH EAST
APC: 6556
PDP: 13579
Ƙaramar Hukumar UHUNMWODE
APC: 5972
PDP: 10022
Ƙaramar Hukumar AKOKO EDO
APC: 22963
PDP: 20101
Ƙaramar Hukumar ETSAKO EAST
APC: 17011
PDP: 10668
Ƙaramar Hukumar ETSAKO CENTRAL
APC: 8359
PDP: 7478
Ƙaramar Hukumar ORHIONMWON
APC: 10458
PDP: 13445
Ƙaramar Hukumar OVIA SOUTH WEST
APC: 10636
PDP: 12659
Rikicin siyasa a jihar Edo
A bana dai, an ta samun rikicin cikin gida a jihar ta Edo a Jam'iyar APC wanda hakan ya sa aka yi ta samun sauyin sheƙa daga APC zuwa PDP.
Rashin jituwa da aka samu tsakanin Obaseki da tsohon shugaban APC kuma tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomhole, ya sa aka hana Obaseki tikitin tsayawa takara a APC sakamakon zarginsa da cewa ba shi da takardun makaranta.
Hakan ya sa Godwin Obaseki ya bar APC ya koma PDP bayan hana shi tikitin tsayawa takarar, inda shi kuma Ize-Iyamu ya bar PDP ya koma APC.
Fasto Ize-Iyamu ya samun goyon bayan Adams Oshiomhole da kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kuma ya taɓa irin wannan takara da Obaseki a 2016, amma kuma lokacin Obaseki na APC, shi kuma Ize-Iyamu na PDP.











