Ƙungiyar Ecowas: Abu biyar da ke gaban sabon shugabanta Nana Akufo-Addo

Asalin hoton, Ghana Presidency
Kungiyar Ecowas ta zabi shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo a matsayin sabon shugabanta.
Shugabannin kasashen yammacin afirka sun zaɓi Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban ƙungiyar a taronsu karo na 57 da suka gudanar jiya a birnin Yamai na Nijar.
Shugaban na Ghana a yanzu shi ya maye gurbin shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou.
Abubuwan da sabon shugaban Ecowas zai mayar da hankali

Asalin hoton, Ghana Presidency
Tsaro
Matsalar tsaro da ke adabar ƙasashen yammacin Afirka na daga cikin muhimman batutuwa da ake saran Nana Akufo-Addo ya mayar da hankali wajen nemo bakin zaren, musamman sabbin barazanar kungiyoyin ta'addanci, rikicin kabilanci da yan fashin teku.
Akwai kuma rikicin siyasar Mali da har yanzu aka gaggara samar da maslaha bayan juyin mulkin sojoji.
Kudin bai daya
Wannan batu ne da har yanzu ake magana a kai, kasashen yammacin afirka na fama da dimbin matsalolin tattalin arziki da kuma na cinikayya wadanan na daga cikin dalilan da ya sa ake ganin samar da wannan kudi zai inganta tattalin arzikin kasasashen da cinikayya.
Zaɓuka
Zaben shugaban kasa da na ƴan majalia a Burkina Faso da Ivory Coast da Ghana da Nijar su ma wasu ƙalubale ne gaban sabon shugaban na Ecowas domin tabbatar da cewa anyi zabe cikin adalci da sahihanci da kuma tabbatar da cewa ba a samu rigingimu siyasa ba a wadanan kasashe.
Alaƙar Ghana da Najeriya
Rigimar da Najeriya ke yi da Ghana kan tsangwamar yan kasuwarta na daga cikin matsalolin da sabon shugaban Ecowas zai yi kokarin shawo kan ta.
Akwai dai rashin kyautawar da Najeriya ke zargin Ghana na yi wa ƴan kasarta da suka hada da: rushe wani gini na ofishin jakadanacin Najeriya a birnin Accra da iza ƙeyar 'yan Najeriya zuwa gida da rufe shagunansu.
Muradan Ecowas kafin 2050
Ya kasance dole sabon shugaban ya taka muhimmiyar rawa da bada tasa gudunmawar a muradun Ecowas na shekara ta 2050.
Ƙasashen yammacin Afirka dai fatan ganin sun inganta rayuwar al'ummarsu da sama musu makoma mai kyau da cigiyar da ƙasashen ka cigaba.
Yadda taron Ecowas din ya kasance
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin Ecowas su mutunta wa'adi da ya kamata su yi a kan karagar mulki kamar yadda kudin tsarin mulki ya shata.

Asalin hoton, Bashir Ahmad
Wannan gargadi na zuwa ne bayan shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara ya yanke shawarar neman wa'adi na uku a zaben watan Oktoba.
Shugaba Buhari ya yi wannan tsokaci ne a taron da shugabanin ƙasashen yammacin suka gudanar.
Kuma galibi batun makale wa da babakere ko nuna jan wuya wajen sauka daga mulki abu ne da ya jima yana ciwa ƙasashen afirka da dama tuwo a ƙwarya, wannan ya sa taron ya taɓo wannan batu.

Asalin hoton, Ghana Presidency
Taron na kwana guda da aka gudanar a jiya litinin, ya samu halarta shugabannin ƙasashe 8, cikinsu harda shugaban Ghana da Senegal da Burkina faso.
Sauran batutuwan da suka tattauna a taron sun hada da matsalolin tsaron Mali. Shugabannin Ecowas sun bukaci a gaggauta mika mulki daga farar hula bayan juyin mulkin soji a ranar 18 ga watan Agusta.
Ecowas dai tuni ta sanyawa sojojin da suka jagoranci juyin mulki takunkumi da kuma bukatar a gaggauta zabe a cikin wannan shekara.

Asalin hoton, Ghana Presidency











