Shugabannin Afrika da suka mutu kan mulki a shekara 22 da suka wuce

Asalin hoton, Reuters
A ranar Talata 20 ga watan Afrilu ne shugaban ƙasar Chadi Idris Deby ya rasu sakamakon raunukan da ya ji a fagen daga.
A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi "ya ja numfashinsa na ƙarshe a yayin da yake kare martabar ƙasar a fagen daga".
shi ne shugaban ƙasa na biyu da ya mutu a Afirka cikin shekarar 2021, bayan shugaban Tanzania John Pombe Magufuli, wanda ya mutu ranar Laraba 17 ga watan Maris yana da shekara 61 a duniya.
Mataimakiyar Shugaban ƙasar Samia Suluhu ce ta tabbatar da mutuwar shugaban inda ta ce ya mutu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.
BBC ta yi nazari kan shugabannin Afirka da suka mutu cikin shekara 20 da suka wuce.
Daga cikin su dai akwai wadanda suka mutu sakamakon rashin lafiya, yayin da wasu kuma kashe su aka yi.
Ga dai jerin sunayen shugabannin da kasashensu da kuma sanadin mutuwar tasu:
- Afrilu 2021: Shugaba Idris Deby na Chadi, shekararsa 68 - An kashe shi a filin daga
- Maris 2021: John Pombe Magufuli na Tanzaniya, shekararsa 61 - Ciwon zuciya
- 2020: Pierre Nkurunziza na Burundi, shekararsa 64 - Bugun zuciya
- 2014: Michael Sata na Zambia, shekararsa 77 - Cutar da ba a bayyana ba
- 2012: Meles Zenawi, firaministan Habasha, shekararsa 57 - Cutar da ba a bayyana ba
- 2012: John Atta Mills na Ghana, shekararsa 68 - Cutar da ba a bayyana ba
- 2012: Bingu Wa Mutharika na Malawi shekararsa 78 - Bugun zuciya
- 2012: Malam B Sanha na Guinea Bissau, shekara 64 - Ciwon suga
- 2011: Mo'ammar Gaddafi na Libiya, shekararsa 69 - 'Yan aware ne suka kashe shi
- 2010: Umar Musa 'Yar aduwa na Najeriya, shekararsa 58 - Matsalar zuciya
- 2009: Joao B Vieira na Guninea Bissau, shekararsa 69 - An kashe shi
- Omar Bango na Gabon, 2009, shekararsa 72 - Kansar hanji
- 2008: Lansana Conte na Guinea, shekararsa 74 - Ciwon suga/matsalar zuciya
- 2008: Levu Mwanawasa na Zambiya, shekararsa 59 - Shanyewar ɓarin jiki
- 2005: Gnassingbe Eyadema na Togo, shekararsa 69 - Bugun zuciya
- 2003: Muhammad H.I Egal na Somaliland, shekararsa 73 - Rashin lafiyar da ba a bayyana ba
- 2001: Kaurent D Kabila na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, shekararsa 61 - Masu tsaronsa sun kashe shi
- 1999: Ibrahim B Mainsara, shugaban Nijar, shekararsa 50 - Masu tsaronsa ne suka kashe shi
- 1999: Sarki Hassan II na Moroko, shekararsa 70 - Cutar numoniya.








