Wutar Lantarki: Shin solar na neman maye gurbin janareto ne a Najeriya?

Asalin hoton, EPA
Matsalar wutar lantarki a Najeriya na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ci wa 'yan ƙasar tuwo a ƙwarya.
Gwamnatoci da dama da suka shuɗe a Najeriya sun sha alƙawuran cewa za su kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a ƙasar, sai dai kowace gwamnati idan ta zo, tana taɓuka abin da za ta iya yi ne ta ƙara gaba.
Rashin wadatar wutar a kasar ya sa jama'a da dama ke nemar wa kansu mafita ta yadda za su samu lantarki a gidajensu da wuraren sana'o'insu.
Akwai jama'a da dama da ke amfani da janareto, sai dai tsadar kudin man fetur ya sa wasu suke haƙura da amfani da janareton su zauna hakan ba wuta.
Amma a halin yanzu, wasu 'yan ƙasar sun fara nemar wa kansu mafita ta hanyar amfani da makamashin samun wutar lantarki ta hanyar hasken rana wanda aka fi sani da solar.
BBC ta tattauna da wani masanin kimiyyar lantarki, Injiniya Ahmad Abubakar, inda ya bayyana alfanun amfani da hasken rana domin samun lantarki.
Injiniya Ahmad ya shaida mana cewa ya shafe kusan shekara 20 yana haɗa solar a gidajen mutane.

Amfanin Solar
Solar, wani abu ne kamar faifai wanda ake ɗora shi a saman rufin kwanon gida, inda faifan yake sauya batiri domin samun wutar lantarki.
Injiniya Ahmed ya bayyana cewa "yanzu haka akwai mutane da yawa a Abuja waɗanda sun yanke wutar gwamnati sun koma amfani da hasken rana domin samun lantarki.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai ya ce ita solar babbar damuwarta ko kuma abin da ya sa mutane ke gudunta, shi ne tsadarta. "Ba kamar janareto ba ne da za ka saya dubu 15 ko dubu 20, ana magana ne na dubu ɗaruruwa.
"Sai dai idan ka riga ka sayi solar, to babu wata maganar sayen fetur yau ko gobe, mutum ya huta, idan ka haɗu da batiri mai kyau sai ka shekara uku ko biyar kafin ka sauya batiri."
A cewarsa, idan kuma mutum bai yi sa'ar batitri mai kyau ba, to mutum zai ta haɗuwa da matsala.
Ya ce hakan kan faru ne sakamakon akwai waɗanda ba su san yadda harkar take ba sai su shiga su rinƙa ɓata musu suna.

Nawa mutum ke buƙata a Najeriya ya haɗa solar?
Injinya Ahmed ya bayyana cewa idan mutum na da akalla 300,000 zai iya haɗa solar a gidansa domin amfani da talabijin da firij da sauran kayan lantarki na gida.
"Akwai dabaru da za mu iya yi wa mutum domin mayar masa da fankarsa ta solar da dutsen guga na solar, akalla mutum zai iya kashe 300,000 zuwa 350,000.
"Idan ka haɗa wannan, ko ba ka da NEPA za ka iya zama a gidanka batiranka su yi maka shekara uku zuwa biyar."
Ya ce shi kuma faifai na solar wanda ake ɗorawa saman rufin gida, ba a sauya shi sai ya kai shekara 20 zuwa shekara 25.

Karancin barazanar hatsari
Injiniya Ahmed ya bayyana cewa "solar na da ƙarancin hatsari ba kamar janareto ba da mutum zai rinƙa tsoron gobarar fetir ko kuma hayaƙi ya yi illa ga mutane ko kuma ka je zuba mai kana haskawa da fitila fetir ya tashi da kai."
Ya ce "tana da ƙarancin barazanar hatsari ba kamar janareto ba, amma duk da haka idan ba a saka ta yadda ya kamata ba za a iya samun matsala," in ji shi.
A cewarsa, ana keɓe ta ne a cikin wani keji a gida, ko a falo ko a wani daki, mutane za su yi ta mu'amala babu wata matsala.

Asalin hoton, Getty Images
Shin janareto na da illa ga muhalli?
BBC ta tattauna da Farfesa Adamu Tanko, wani masani kan kimiyyar muhalli a Najeriya domin jin ko janareto da ke bayar da wutar lantarki na da wata illa ga muhalli.
A cewar Farfesan, hayaƙin janareto ko na mota ko kuma wasu injuna na masana'antu masu fitar da hayaƙi na da illa ga muhalli da kuma lafiyar ɗan adam.
A cewarsa, "batun illa ga lafiyar ɗan adam likita ne zai yi bayani amma ga muhalli, hayaƙi na taimakawa matuƙa wurin samun ɗumamar yanayi a duniya".
Ya ce idan ana fitar da wannan hayaki, yana ƙara samar da ɗumamar yanayi, kuma akwai wata shigifa da ke kare duniya daga shigowar hasken rana wanda ake kiransa ozone layer, a cewarsa, wannan hayaƙi da yake shiga ciki yana rage masa ƙarfi ko kuma zaizaye shi.
Ya ce idan aka ci gaba da samun irin wannan hayaƙi to za a samu nakasu da yakin da gwamnatocin ƙasashe suke yi da ɗumamar yanayi.











