Black Lives Matter: 'Za mu ɗora a kan gwagwarmayar iyayenmu'

Diyar Martin Luther King da Malcolm X da Kwame Nkrumah na fafutikar kare hakkin baƙar-fata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Diyar Martin Luther King da Malcolm X da Kwame Nkrumah na fafutikar kare hakkin baƙar-fata

Amurkawa baƙaƙen fata na gudanar da wata gagarumar zanga-zangar neman 'yancinsu wadda ta yi daidai da bikin cika sheekara 57 da yin shararren jawabin nan na Martin Luther King Jr na "I Have a Dream" wato "Ina da Buri".

Macin da aka shirya na "Get Your Knee off our Necks" wato "Ku Cire Ƙafarku Daga Kan Wuyana" a Washington ranar 28 ga watan Agusta ya ƙara rura wutar zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi don yin Allah-wadai da kisan baƙar fata da 'yan sanda ke yi.

Dr Bernice King da Farfesa Ilyasah Shabazz da Samia Nkrumah dukkaninsu 'ya'yan shahararrun masu fafutikar 'yancin baƙar fata ne.

A wannan hirar ta musamman da BBC, sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda za su ci gaba da ayyukan da iyayensu suka fara da kuma yadda abubuwan ke ci gaba da faruwa a yanzu.

Dr Bernice King - 'Yar Martin Luther King-

Shugabar cibiyar King Center. Mahaifina ne ya yi jawabin nan na "I Have A Dream", wanda aka kashe shi a shekarar 1968.

Dr Bernice King za ta ci gaba da fafutikar da mahaifinta ya fara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dr Bernice King za ta ci gaba da fafutikar da mahaifinta ya fara

"Ina ganin mun samu gagarumin ci gaba a cikin ƙanƙanin lokaci.

Mahaifiyata ta sha yin magana kan sasantawa amma ni tunani na shi ne: "Ta ya ya wani zai kashe mahaifina haka kawai a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da an zauna lafiya a duniya?"

Shekara 57 kenan da yin zanga-zangar "I Have A Dream"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekara 57 kenan da yin zanga-zangar "I Have A Dream"

Hakan ya sa nake jin haushin kowa musamman fararen fata.

Har sai da ta kai ga abin yana matuƙar damu na. Daga baya na fara tambayar kai na cewa shin ya kamata na ci gaba da zama haka ina zaluntar kai na - saboda tsana ce take jawo hakan.

A studio portrait of the Rev. Bernice Albertine King

Asalin hoton, Getty Images

Na ga an samu sauyi ta hanyar yadda ake ɗaukar baƙaƙen fata da kuma yadda ake siffanta su."

Farfesa Ilyasah Shabazz - 'Yar Malcolm X

Farfesa Shabazz marubuciya ce kuma mai fafutikar nema wa mutane ilimi. Mahaifinta sananne ne kuma shugaba a lokacin neman 'yanci. An kashe shi a 1965.

Ilyasah Shabbaz ta rubuta littafi mai suna "Growing Up X"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ilyasah Shabbaz ta rubuta littafi mai suna "Growing Up X"

"Mun ga yadda aka yi wa George Floyd kisan wulaƙnci, ba mamaki saboda muna zaune ne kawai a gida. Kuma mun ga mace-mace iri-iri.

Sai yanzu mutane suke fahimtar abin da Malcom X ya ke faɗa. Kuma suna fahimtar cewa Malcom X mutum ne mai tausayi da ya san ya kamata kuma mai neman mafita domin kowa ya rayu cikin aminci, ya samu ilimi, ya bayar da gudummawa a tattalin arziki.

Suna fahimtar cewa waɗanda ke aikata waɗancen kashe-kashen su ne kuma suke bayar da labaran ko wane ne Malcom X - labaran ƙarya.

Kare haƙƙin mata na kan gaba a yaƙin da Shabbaz ke yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kare haƙƙin mata na kan gaba a yaƙin da Shabbaz ke yi

Samia Nkrumah - 'Yar Kwame Nkrumah

Samia Nkrumah shugabar jam'iyyar Ghana's Convention People's Party ce a Ghana. Mahaifinta tsohon shugaban Ghana ne kuma shahararre wurin kare haƙƙin Afirka.

'Yar shugaban ƙasar Ghana na farko na ci gaba da fafutikar haɗa kan 'yan Afirka da kare haƙƙin mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar shugaban ƙasar Ghana na farko na ci gaba da fafutikar haɗa kan 'yan Afirka da kare haƙƙin mata

"Abin alfarma ne yadda nake ci gaba da alaƙanta kaina da ayyukan mahaifina a siyasance. Har abada zan ci gaba da ɗabbaƙa manufofinsa kan Ghana da duniya baki ɗaya.

A yanzu ne ya fi kamata a Afirka ta haɗa kai sama da shekara 50 ko 60 da suka wuce. Haɗin kan 'yan Afirka ba shi kaɗai ake nema ba, yana nufin su karɓi mutuncinsu da samun adalci.

Samia Nkrumah during a visit to Milan

Asalin hoton, Getty Images

Fafutikar 'yancin kai a ƙasashemmu na Afirka na da alaƙa da 'yan Afirka a duk inda suke. Fafutikar baƙaƙen fatar Amurka da fafutikar wariyar launin fata. Waɗannan abubuwa duka na da alaƙa da juna.

Za a cimma waɗannan abubuwa cikin sauri idan 'yan Afirka biliyan 1.5 suka yi aiki tare domin samun adalci.

Iyayenmmu da kakannimmu sun yi fama kafin mu samu 'yanci a siyasance da kuma mutuntaka.

Saboda haka, lokacimmu ne 'yan Afirka a duk inda muke, tare da taimakon duniya baki ɗaya, mu tabbatar da samun 'yancin kammu na tattalin arziki.