Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Amurka : Trump ya karbi tikitin yin tazarce a karo na biyu
Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya sake tsayawa takara don yin tazarce karo na biyu a karkashin jam'iyyar Republican.
Ya fadawa taron magoya bayansa da suka halarci ganin karbar takarar tasa cewa yana da kwarin guiwar ci gaba da kasancewa a kan mulki har nan da shekaru hudu masu zuwa.
Ya jaddada abin da ya saba fada na kushe abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrat Joe Biden, wanda ya ce zai ruda dadadden mafarkin da kasar ta jima tana yi.
Mr Trump, ya kuma yi alkawarin sake gina tattalin arzikin kasar wanda annobar korona ta gurgunta, in da yace kafin zuwan cutar ya samar da tattalin arzikin da babu wani shugaba da ya taba samar da irinsa a tarihin kasar.
Ya kuma yi wa 'yan kasar albishiri din cewa za a samar da rigakafin cutar korona daga nan zuwa karshen shekara.
Sai dai babban taron jam'iyyar na wannan karon ya sha ban-ban da tsarin siyasar Amurka, in da a wannan karon aka rika amfani da gine-ginen gwamnati, da kuma nuna goyon baya ga shugaba Trump da iyalansa.
Ita ma mai dakinsa Melania Trump da mataimakin shugaban kasa Mike Pence, duk sun gabatar da nasu jawabin ne daga fadar shugaban kasa.
Wannan ce rana ta karshe ta taron jam'iyyar, bayan da jam'iyyar Democrat ta yi nata a makon da ya gabata.
A watan Octoba kuma Mista Trump na Republican da Joe Biden na Democrat za su bayyana tare don tafka muhawara, yayin da zai rage wata daya kacal kafin zabe.