Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Afrika: 'Akwai alamun nasara' ganin yadda cutar ke raguwa
Yawan masu kamuwa da cutar korona da ake samu duk mako a Afrika ya ragu a makon da ya gabata, a cewar Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Afrika (Africa CDC).
An rinka samun masu kamuwa da cutar 10,300 duk rana a makon da ya gabata, inda ya ragu daga 11,000 na mako biyu da suka gabata.
Shugaban CDC, Dokta John Nkengasong, ya ce ''alama ce ta kyakkyawan fata''.
Afirka na da waɗanda suka kamu da cutar har 1,147,369, fiye da rabinsu kuma a Afirka Ta Kudu suke, sannan kusan mutum 26,000 ne suka mutu.
Dokta Nkengasong ya ce yana cike da fatan cewa abin na raguwa a hankali, amma ya ƙara da cewa ya yi wuri sosai - wannan ƙwayar cutar sai an bi ta a hankali don tana da saurin yaɗuwa.
''Mun ɗauki wannan labarin a matsayin mai daɗi amma sai an yi taka tsan-tsan, inda ya bayyana cewa ba ya so mutane su yi saurin watsi da matakan kare yaɗuwar cutar.
Ya buƙaci mutane da su ci gaba da ƙoƙari wajen kare yaɗuwar ƙwayar cutar, musamman batun cewa mutane na buƙatar ci gaba da sanya takunkumi, da bayar da tazara da kuma yin gwaji.
Shin ya kamata Afrika ta yi murna?
Anne Soy, BBC News, Nairobi
Bayan yawan waɗanda suka kamu da cutar korona a Afrika ya yi sama, raguwar da aka samu ta masu kamuwa da ita a duk mako ya zamo wani abin kwantar da hankali.
Amma sai dai ana buƙatar yin matuƙar taka tsan-tsan kan lamarin.
An samu ƙaruwar yin gwaji sosai a watannin da suka gabata inda aka yi wa fiye da mutum miliyan 10 gwaji zuwa yanzu, a cewar CDC.
Kusan kashi ɗaya cikin 100 kenan na yawan al'ummar ƙasar.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta alaƙanta raguwar da aka samu a Afrika da raguwar masu kamuwa da cutar a Afirka Ta Kudu a ƴan kwanakin nan.
Amma rashin yin gwaji sosai a nahiyar na nufin har yanzu ba a san taƙamaimai yadda annobar ke yaɗuwa ba.
Don haka ya yi wuri a yanzu a yi hasashen ko wannan raguwar da ake samu ta sabbin masu kamuwa da cutar zai ci gaba a haka a nahiyar.
Dokta Nkengasong ya kuma ce an yi wa fiye da mutum miliyan 10 gwaji a faɗin nahiyar, inda ƙasar Afirka Ta Kudu ta zama kan gaba wajen yin mafi yawan gwajin.
Sai dai yawan masu kamuwa da cutar da mace-macen da ake samu bai kai na wasu yankunan duniyar ba kamar Turai da Latin Amurka da Amurkar kanta, wacce ita kaɗai tana da masu ɗauke da cutar fiye da 5,500,000, amma wasu ƙwararru sun yi gargaɗi cewa wataƙila akwai masu ɗauke da cutar sosai a Afrika sai dai rashin yin gwaji ya sa ba a gano su.