Coronavirus a Gombe: Dalibai 'yan mata tara da ke rubuta WAEC sun kamu da cutar

Hukumomi a jihar Gombe da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce dalibai tara da ke rubuta jarrabawar WAEC sun kamu da cutar korona.

Kwamishinan ilimi na jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan daliban sun fito ne daga wasu jihohi da suke hulda da su a tsarin musayar dalibai.

Ya kara da cewa an gano su ne sakamakon matakan da gwamnatin jihar ta dauka na yi wa dukkan dalibai da malamai da dukkan ma`aikatan da ke makarantun jihar gwaji.

"A makarantar mata na Government Secondary School, Doma, mun samu dalibai tara da suka kamu da cutar korona kuma mun kai su Specialist Hospital. Haka kuma a makarantar mata ta Kumo, can ma mun samu daliba daya da ta kamu da cutar korona," in ji shi.

Dr Habu ya ce daliban da su gudanar da jarrabawarsu a cibiyar da aka killace su, yana mai cewa za a kai musu masu sanya ido domin ganin cewa ba a samu matsala yayin da suke rubuta jarrabawar ba.

A farkon mako, an gano wani dalibi a jihar ta Gombe wanda ya kamu da cutar korona.

Mutum 684 jumulla suka kamu da cutar ta korona a jihar Gombe ya zuwa ranar 19 ga watan Agusta.