Coronavirus a Nepal: Yaya lafiyar matan da ke jinin al'ada take a lokacin dokar kulle?

Asalin hoton, VSO/P Mathema
A yankunan karkara na kasar Nepal inda ake tsangwamar matan da suke jinin al'ada, masu aikin sa-kai suna taimaka wa 'yan mata da manyan mata domin magance kalubalen da suke fuskanta lokacin kulle, saboda su kasance cikin tsafta lokacin da suke haila.
Wurin da ake kallon jinin al'ada a matsayin haramun - ko chhaupadi - ana haramta wa 'yan mata da manyan mata taba abubuwan ayyukan gida, kuma ana killace su ne a wasu bukkoki tsawon kwanakin da suke jinin al'ada.
A wasu gidaje lokacin da aka sanya dokar kulle sakamakon cutar korona, wasu 'yan mata suna fuskantar sabbin kalubale na samun audugar mata.
Masu aikin sa-kai na kungiyar Voluntary Service Overseas' Sisters for Sisters' Education sun samar da mafita lokacin barkewar annobar korona, inda suka rika rarraba fakiti-fakiti na kayan tsaftace jiki ga 'yan mata kusan 3,000 a lardunan Surkhet, Lamjung, Dhading da kuma Parsa na kasar Nepal.
Fakiti-fakitin na kunshe da sabulai, da tawul, da burushin goge baki da audugar mata da ake amfani da ita fiye da sau daya, da kamfai, da abubuwan yanke farce da kuma ruwan sinadarin chlorine.
Daya daga cikin 'yan matan da suka ci moriyar wannan kungiya ta bayyana halin da ta shiga lokacin da take jinin al'ada a lokacin kulle tare da 'yar uwarta.


Asalin hoton, VSO/P Mathema
Anjali Patel, 'Karamar 'yar uwata'
Anjali, mai shekara 15, tana aji hudu na firamare lokacin da masu aikin sa-kai suka soma tallafa mata.
"Lokacin ina da shekara 10, ba kasafai nake zuwa makaranta ba domin ina shagala wajen ayyukan gida," in ji Anjali.
"Su ma iyayena ba su san muhimmancin tura ni makaranta ba.
"Babbar yayata Muni ce ta zo ta shaida wa mahaifana muhimmancin aika ni makaranta.

Asalin hoton, VSO/P Mathema

Asalin hoton, VSO/P Mathema
"Tasiri cutar korona ya shafi karatuna sakamakon dokar kullen da aka sanya a fadin kasar kuma hakan ya sauya rayuwarmu sosai," a cewar Anjali.
" An gaya mana mu zauna a gidajenmu kuma kada mu gana da kawasyenmu da manyan 'yan uwanmu.
"Ta hanyar wayar tarho, Muni ta ilimantar da mu kan yadda za mu dauki matakan wanke hannayenmu kuma kada mu fita daga gida sai dai idan hakan ya zama wajibi, domin hakan zai kare mu daga kamuwa da cutar korona.
" Ta rika kiranmu a wayar tarho tana nuna mana yadda za mu kasance cikin tsafta lokacin jinin al'ada.
"Lokacin dokar kulle, ban iya sayen audugar mata ba. Lokacin da muke makaranta mukan samu audugar, amma dokar kulle ta hana mu zuwa makaranta.


Asalin hoton, VSO/P Mathema
Muni Gupta, 'Babbar 'Yar uwata'
A matsayinta na mai aikin sa-kai wacce take bayar da shawara ga 'yan mata 11 a kauyensu, Muni tana wayar da kan jama'a kan cutar korona, da kuma yadda 'yan mata za su rika tsafta lokacin kullen korona.
"Lokacin dokar kulle, Ina yawaita tattaunawa da kannena mata ta hanyar wayar tarho," in ji Muni.
"Tun lokacin da aka samu masu dauke da Covid-19 a kauyenmu, mutane suka fada cikin fargaba.
" An kyale ni na ziyarci kawayena kalilan da ke kusa da gidanmu ta yadda zan wayar musu da kai kan wanke hannu da kuma sanya takunkumi.

Asalin hoton, VSO/P Mathema
"Ta hanyar kungiyar [Sisters for Sisters' Education project] mun samu horo kan yadda za mu yi amfani da audugar mata fiye da sau daya a gidajenmu, kuma hakan ya sa na koyawa 'yan gidanmu da kuma 'yan matan kauyenmu," a cewar Muni.

Asalin hoton, VSO/P Mathema

Asalin hoton, VSO/P Mathema
" Ina alfahari da jin cewa al'ummar kauyenmu sun gamsu da aikin da na yi kuma sun karfafa min gwiwa."

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.











