Ranar Matasa Ta Duniya: Nazari kan kalubalen da matasa ke fuskanta a Najeriya

Wannan makala ce da matashiya Ummulkhair .A. Musajo ta rubuta albarkacin ranar matasa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a duk ranar 12 ga watan Agusta.
Ummulkhair .A. Musajo daliba ce a jami'ar Nile University da ke Abuja Najeriya, inda kuma take tare da sashen Hausa na BBC domin sanin makamar aiki.
Lokacin da nake sauraren Sajida tana ba da labarin takaicinta na yi wa kasa hidima wato NYSC, nan na fahimci yadda gwamnati take rashin kyautata wa matasanta.
"Cabdi," abin da kawai na iya fada kenan, yayin da take ajiyar zuciya tana baƙin ciki.
Na yi mamakin kalubalen da ta fuskanta, ko kuma na ce ina matukar mamakin abin da matasa za su fuskanta nan gaba.
"Don Allah duba yadda fatan matasan da suka kammala jami'a na samun rayuwa ta gari yake dusashewa a duk shekara. Tamkar dai an watsa maka ruwan sanyi ne kana tsaka da barci. Nan da nan za ka rude, ka fuskanci cewa duniyar nan fa ta mai rabo ce!" A ƙarshe na sami damar faɗi bayan na nutsu.
"Saboda mun ki yin tsari, mun ki fahimtar yadda tsarin da muka amfani da shi ya gaza kuma muka ƙi gyarawa," a cewar Sajida.
Ina kokarin yin tunanin hanyoyin da za mu iya inganta al'amura a Najeriya amma abin da kawai nake tunani shi ne abin da wata jami'a a hukumar NYSC ta gaya wa Sajida bayan ta mika mata tufafin da suka mata yawa.
"Sai ki nemi wata da ke da karamin wando ki yi musaya da ita," in ji ta.
"Allah Ya agaza mana," abin da ya fito daga bakina kena.
Matasa su ne kashin bayan kowacce al'umma; su ne ke motsi da girgiza ginshiƙai, kuma su ne waɗanda suke yi da gaske a cikin canjin da ake buƙata.
Kididdiga ta nuna cewa matanan Najeriya su ne sama da rabin (53%) na yawan mutanen Afirka don haka matsalolin da suke fuskanta suna kawo koma-baya a ci gaban zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasar.
A wannan labarin Ina shirin bayyana wasu matsalolin da ke addabar matasa a Najeriya. Kuma na tambayi mutane game da matsalolin da matasa ke fuskanta a Najeriya.
Cin hanci
Duk lokacin da mutum ya yi tunanin Najeriya da matsalolinta, abu na farko da zai shiga zuciyarsa shi ne cin hanci da rashawa da suka yi mata katutu shekaru da shekaru. Babu wanda wannan lalacewa ta fi shafa tamkar matasa domin su ne ba sa samun damar amfani da kwarewarsu wajen aiwatar da ayyukan ci gaba.
Tsofoffin shugabanni na Najeriya su ne 'yan siyasa masu hadama, wadanda tsawon shekaru sun ki bayar da dama ga matasa kamar dai yadda su ma suka ci moriya lokacin da suke wannan matsayin.
su ne ke yanje shawara kan abubuwan da za su shafi matasa ba tare da la'akari da irin rayuwar da suke son gabatarwa ba.

Rashin aikinyi

Asalin hoton, Getty Images
Matasa suna kokawa ta hanyar karatunsu tare da fatan neman aiki mai inganci da ma'ana wanda za su yi amfani da shi don biyan bukatun kansu da danginsu amma ba haka lamarin yake ba.
Tsoffinmu sun ki yin ritaya. Sun ci gaba da karyata shekarun su domin rike aikinsu alhali 'ya'yansu, musamman masu karatun digiri suna yawo ba tare da aiki ba.
Tunda an ce 'zaman kashe wando yana sa miyagun tunani' shi ya sa wasu lokutan matasa kan shiga ayyukan masha'a kamar sace-sace, yahoo-yahoo, tsafi da sauransu.
Mun ji daga wurin Abdulrahman Mahmoon akan matsalar da ya fuskanta a matsayinsa na matashi a Najeriya.
"Babban kalubalen da na fuskanta a matsayina na matashi dan Najeriya shi ne rashin aikin da ya dace da irin karatun da na yi. Na yi karatu har zuwa matsayin digiri kuma na gama jami'a da lambar yabo amma a wajen fannin neman aiki sai na ga mutanen da ba su samu irin sakamakon da nake da shi ba sun sami aikin bayan ni an ce mun na yi hakuri," in ji shi
"Na rasa gane kan al'amarin, kuma yana damu na sosai. Alhamdulillah ban tsaya jiran samun aiki ba, na kama gaba na kuma ina aikin da nake samun rufin asiri; amma gaskiya harkar aiki a kasar nan babban abun takaici ne."

Matsalar shaye-shaye
Matsalar shaye-shaye tana ci gaba, kuma har yanzu babbar matsala ce da ke addabar matasan Najeriya.
Alkaluma sun nuna cewa wasu matasa sun rungumi shaye-shaye ne domin huce takaicin matsalolin rayuwa lamarin da kan tagayyara su.
Matsalar kwayoyi da shan wiwi har yau cuta ce da ke aukuwa tsakanin matasa a yayin da ake hana mutum guda, biyu zasu taso. Hakan ya shafi mata da maza.
"A cikin matsololin da matasa ke fuskanta, shaye-shaye duk ya fi muni. Matasa, mata da maza sun koma ga dogaro ga kwayoyi da sauran abubuwa masu cutarwa wadanda sun zama abin samu cikin sauki a duniya," Faraz Muhammad ya ce.
"Ba wani sabon abu ba ne domin ya dade yana faruwa, kuma wadatar fahasa da kuma sha'awar matasa, sun sa ana sauƙin samun yanzu fiye da shekaru goma da suka gabata," a cewarsa.

Lafiyar kwakwalwa
Lafiyar kwakwalwa shi ne babban batun lafiyar jama'a wanda ke buƙatar kulawa mai kyau.
Mutane a Najeriya suna wasa da batun lafiyar kwakwalwa, ana ganin shi kamar aljanu ne ko yanayin jujjuyawa, kuma saboda wannan yana da matukar wahala ga matasa su bayyana matsalolinsu.
Wata babbar matsala a kan wannan batu ita ce galibin masu fama da cutukan da suka shafi damuwa ba sa samun kulawa lamarin da kan sa su zautu sosai.
Na tattauna da Khadijah Uthman, wata matashiya da ke samun kwarewa a aikin likita, a kan wannan matsalar, ta ce "Idan mutane sun ce 'Lafiyar Kwakwalwa' yawanci tunaninsu na zuwa ta wurin damuwa da zakuwa; mun dauka cewa idan mutum ba ya fama da cutukan da aka fi sani, to wannan mutumin yana da lafiya gaba ɗaya."
Ta kara da cewa: "Yawancin mu ba mu da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa. Don haka, ina ganin wannan matsalar ciwon kwakwalwa kalubale ne da muke fuskanta, kuma abin da ya fi muni shi ne ba mu san shi ba."
Domin a janye matasan Najeriya daga kalubalen da suke fuskanta dole sai an samar musu da ayyukan yi ta yadda za su daina zaman banza. Dole ne a ja su a jiki kuma a samar da su ta hanyar abubuwan alheri. Wannan zai haifar da ci gabansu da na wannan ƙasar, har ma a duk faɗin duniya.












