Juventus ta kori kocinta Maurizio Sarri

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta sallami mai horarwarta Maurizio Sarri bayan kakar wasa ɗaya kacal.

Sarri ya jagoranci Juventus lashe kofin Serie A na tara a jere amma Lyon ta cire su daga Champions League a zagayen 'yan 16 a daren Juma'a.

Juve ce ta cinye wasan da ci 2-1 a birnin Turin amma Lyon ce ta yi gaba sakamakon ƙwallon da ta zira a gidan Juve.

Sarri ɗan Italiya mai shekara 61, an naɗa shi ne kan yarjejeniyar shekara uku bayan ya shekara ɗaya a Chelsea.