Zaben Belarus: Matan da suka jingine bambancin siyasa domin yakar shugaban kasa

Daga hagu zuwa dama,Maria Kolesnikova, Svetlana Tikhanovskaya da kuma Veronika Tsepkalo

Asalin hoton, Viktor Babaryko Media Team

Bayanan hoto, Mata ukun da suka hade kansu don yakin nema zaben shugaban kasa a BelarusT

Mata ukun da suka sadaukar da komai domin siyasa.

Svetlana Tikhanovskaya, Veronika Tsepkalo da kuma Maria Kolesnikova sun hada kai domin su jagoranci wani kampe na zama shugaban kasa a babban zaben Belarus da za a yi a cikin watan da muke ciki na Agusta.

Idan har suka samu nasara to Tikhanovskaya ce za ta kasance shugabar kasa.

Ta yanke shawarar maye gurbin mijinta Sergei Tikhanovsky bayan an kama shi an kai shi gidan yari sannan kuma aka hana shi takarar.

Ta sha fuskantar barazana daga mahukuntan kasar a kan za a kwace 'ya'yanta daga wajenta idan har ta ci gaba da takarar amma kuma hakan bai sanyaya mata gwiwa ba.

Sun hada hannu da karfe tare da Veronica Tsepkalo, wadda aka haramta wa mijinta takarar shugaban kasa da kuma Maria Kolesnikova, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasar da aka kai a gidan yari Viktor Babaryko.

Manufarsu ita ce su lashe zaben 9 ga watan Agustan da za a yi a kasar sannan kuma su kawo karshen mulkin Alexander Lukashenko da ya shafe shekara 26 yana yi.

Mutanen kasar sun shiga sahun kampe din da ake yi don nuna goyon bayan 'yar takara Svetlana Tikhanovskaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata da dama sun shiga harkar siyasar Belarus a bana ba kamar a baya ba

Wata mai sharhi a kan al'amuran da suka shafi siyasa a Belarus, Yana Lyushnevskaya ta shaida wa BBC cewa ba wani abu ne ya sa wadannan mata uku suka hade kansu ba illa yanayin siyasar kasar.

Ta ce: " A kusan shekara 30 da ya yi yana mulkin kasar, babu abin da shugaba Lukashenko yake kiran mata illa kawai ya ce babban aikinsu shi ne su kasance matan aure da iyaye sannan kuma masu kula da gida".

Mr Lukashenko wanda aka fara zaba tun a watan Yulin 1994, a yanzu yana neman sake darewa mulkin kasar ne a karo na shida, har ma yana cewa al'ummar Belarus ba su shirya zabar mace shugaba ba, kuma kundin tsarin mulkin kasar ba na mata ba ne.

To amma kuma bai san abin da ya fada zai ja masa bore ba, inda daga baya ya fito ya yi bayani a kan kalaman nasa ya ce ba wai yana kaskantar da mata ko kuma ba ya girmama mata ba ne.

Ya ce: "Abin da kundin tsarin mulkinmu ya kunsa ga namiji zai sha wuya wajen mulkar kasa, ballantana mace, idan har mace ta ce za ta karbi shugabancin kasarmu to lallai wata rana sai ta yanke jiki ta fadi".

Sabon tsari a siyasar Belarus

Dandazon mutane na daga hotunan Svetlana Tikhanovskaya, Veronika Tsepkalo da kuma Maria Kolesnikova suna nuna goyon bayansu a kan manufarsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar 9 ga watan Agusta za a yi zaben shugaban kasa a Belarus

Gangamin hadin gwiwar da matan uku suka jagoranta ya zamo wani abin tarihi a Belarus.

Hotunan matan uku da ake dagawa a wajen gangamin wata alamace ta yadda za a kalubalanci shugaba Lukashenko, inji Lyushnevskaya.

Za a iya cewa dukkansu sabbin fuska ne a siyasa, amma kuma suna da kwarewa a kan siyasa da ma al'amuran da suka shafi rayuwa.

Tikhanovskaya ta ce: "Mai gidana Sergei Tsikhanovsky ya hada kan mutane, don haka muka yanke shawara a kan muma mu hada kai don cimma bukatunmu", wannan shi ne sakon da ta fara yi a bainar jama'a.

Sergei, fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta ne, an kuma haramta masa takarar shugaban kasa sannan aka kulle shi a gidan yari bayan an zarge shi da kitsa wata zanga-zanga.

Idan har ta samu nasara, Tikhanovskya ta ce, tana so ta gudanar da zabe ba tare da magudi ba, sannan za ta saki fursunonin siyasa ta kuma dawo da amfani da kundin tsarin mulkin kasar na 1994, wanda ya rage wa'adin shugaban kasa a kan mulki da kuma takaita yawan sake neman zaben da mutum zai yi.

Fatan samun ci gaba mai dorewa a Belarus

Matasa sun bi sahun zanga-zangar da mata ke yi domin nuna goyon bayansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekaru 26 ke nan babu wanda ke samun nasara a zaben shugaban kasa a Belarus sai Lukashenko

Veronika Tsepkalo, matar dan takarar da aka yi watsi da takararsa wato Valery Tsepkalo, ta amince.

Mai gidanta wanda tsohon jakadan kasar ne a Amurka, an taba kallonsa a matsayin daya daga cikin masu yi wa shugaba Lukashenko barazana, amma kuma yana daga cikin mutum taran da hukumar zaben kasar ta ga ba su dace da tsayawa takarar shugaban kasar Belarus ba.

A yayin gangamin neman zaben da suka yi a Minsk, Veronica Tsepkalo, ta zargi shugaba Lukashenko da janyo raguwar yawan al'ummar kasar.

Ta ce: "Matasanmu na tafiya zuwa wasu kasashe inda iyalansu ke nemar musu inda za su samu rayuwa mai kyau saboda akwai 'yanci a can".

"Akwai 'yancin bayanai da kudi da kuma abu mai muhimmanci shi ne fata, wanda a Belarus babu wadannnan duka, gaskiya muna so mu kawo sauyi a kan wannan".

To amma a bangaren Maria Kolesnikova ba haka abin ya ke ba.

Ita mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa Viktor Babaryko ce, wani fitaccen ma'aikacin banki wanda ake ganin zai iya gogawa da Lukashenko.

A lokacin da aka tursasa masa janyewa daga takarar bayan a kulle shi a gidan yari saboda zargin almubazzaranci da sama da fadi da wasu kudade, sai ta yanke shawarar maye gurbinsa sannan ta hade da sauran matan.

A lokacin, tawagar kungiyar Tarayyar Turai a Belarus ta ce matakin hukumar zaben kasar bai dace da yanayin dimokuradiyyar gaskiya da adalci ba.

Duk da yake matan uku sun fito daga jam'iyya daban-daban, kowacce na bayar da gudunmuwarta a kan abubuwan da take gani za su kawo sauyi a bangaren siyasa da cin hanci da rashawa da kuma yadda za a ciyar da kasa gaba.

Babbar gwagwarmaya

Matan da suke son kawo sauyi a da hadin kai a siyasar Belarus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matan da suke son kawo sauyi da hadin kai a siyasar Belarus

Lyushnevskaya ta ce yakin neman zaben da matan uku ke yi ya sanya shauki a zukatan 'yan kasar da ba su damu da siyasa ba saboda shekarun da aka shafe ana magudi a zaben kasar.

To sai dai kuma akwai fargabar cewa ko yunkurin matan na son kawo sauyi a siyasar Belarus din zai yi tasiri.

Ana ganin dai ko da matan ba su samu nasara ba, sun kafa tarihi, sannan kuma sun kawo hadin kai a wani bangare na siyasar kasar.

Kuma masu suka na ganin cewa, ba lallai ba ne yakin neman zaben shugaba Lukashenko ya yi armashi a wannan karon.