Coronavirus: Me ya sa maza ba sa sanya takunkumin rufe fuska sosai?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Bayan mita da korafi da ta yi ta yi a baya, Monica ta dauki mataki.
Mijinta Eduardo ba ya son sanya takunkumi a daidai lokacin da Covid-19 ke kara ta'azzara a Brazil - kasa ta biyu da ke da yawan wadanda cutar ta kashe a duniya bayan Amurka.
Monica ta yanke shawarar barin gidan mijin ta koma gidan iyayenta tare da dansu mai shekara bakwai.
"Ina da matsalar ciwon asma don haka ina cikin hadarin kamuwa da wannan cuta. Amma mai gidana gani yake kamar na taɓu," ta shaida wa BBC.
"Dalilinsa na rashin sanya takunkumi shi ne ko da yabar gida ai ba ya shiga cikin jama'a."
"Kwata-kwata ba ya tunanin yana yunkurin jefa ni cikin hadari ne ni da ɗanmu," in ji Monica.
Da yawa daga cikin maza sun mutu sakamakon korona.... amma har yanzu da yawa ba sa sanya takunkumi
Ba mu sani ba ko wasu ma'auratan a duniya na cikin irin wannan dambarwa - amma labarin Monica da Eduardo mijinta ya fi kama da banbancin da ke da akwai a wajen jinsin halittarsu lokacin annobar.

Asalin hoton, Getty Images
Ya zuwa ranar 9 ga watan Yuli sama da mutum miliyan 12 a fadin duniya sun kamu da wannan cuta ta korona kuma ta kashe kimanin mutum 550,000, in ji jami'ar jami'ar Johns Hopkins mai tara bayanai kan cutar.
A duka kasashen da aka tattara wadannan bayanai an fi samun mutuwar maza fiye da mata.
Haka zalika bayanai sun nuna cewa maza sun fi watsi da sanya kayan kariya da kuma takunkumi - irin kuma wannan dabi'ar aka rika ganin mazan na yi lokacin sauran annoba a baya.
Sanya takunkumi na daga cikin shawarwarin masana kiwon lafiya domin dakile yaduwar annobar korona.
Amma an samu sauyin bayanai a watannin baya - bayan samun wasu sakamakon bincike da masana suka yi.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta goyi bayan a rika amfani da takunkumi a matsayin wasu dabarun kauce wa Covid-19, duk da cewa takunkumi na da inda yake iya amfani amma sun ce a rika sanyawa musamman a wuraren da ba da tazara yakan zama abu mai wahala.
Jin isa da nuna fifiko
Idan har takunkumi zai iya taimakawa wajen yaki da cutar korona, me ya sa maza ba su damu da sanya shi ba?

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike ya gano cewa maza na jin sanya takunkumi abin kunya ne kuma wata alama ce ta rauni".
"Wannan ya fi faruwa a kasashen da ba su mayar da sanya takunkumi dole ba," in ji Valerio Capraro, wata babbar malama a tsangayar tsimi da tanadi ta jami'ar Middlesex.
Binciken ya nuna sha'awar mata ta sanya takunkumi "a bainar jama'a ta ninka ta mata".
Other studies have consistently shown that men are also less compliant towards hand-washing, one of the basic hygiene measures to help prevent the spread of diseases - with one recent poll finding that 65 percent of women but only 52 percent of men say they are washing their hands regularly.
Wani binciken kuma ya nuna yadda maza ba sa ba da haɗin kai ga dokar wanke hannu, daya dag cikin manyan matakan kariya game da wannan annoba - inda bincike ya nuna kaso 65 na mata na wanke hannu yayin da kaso 52 ne kawai na maza ke wanke hannu a kai-a kai.
Yawan sanya takunkumi karanci mace-mace
An tsammanin amfanin takunkumi zai karu, kamar yadda bincike ya nuna ana iya daukar cutar korona ta iska kuma za ta iya makalewa jikin 'yan kananan abubuwa da ba ma gani maimaikon furkaki da a kan iya samu ko fitar cutuka lokacin da mutane suka yi tari ko atishawa.
Kuma wani bincike da ba a kai ga wallafa shi ba aka yi a Japan ya yi ikirarin cewa akwai alaka tsakanin takunkumi da yawan mace-macen da ake samu a kasashen 22.

Asalin hoton, Getty Images
Wani sharhi daga wani bincike da cibiyar YouGov da Daisuke Miyazawa da kuma Gen Kaneko ya gano kasashen da mutane ke yawan sanya takunkumi na da karancin mace-mace da ba su kai miliyan daya ba.
Wani bincike da ya gudana a Burtaniya ya nuna kasashen 22 da aka fi samun mace-mace sakamakon annobar korona maza na da karancin amfani da takunkumi a cikinsu.
Shin wani abu na ruɗar maza ne?
Christina Gravert wata kwararriya kan kimiyyar halayyar ɗan adam da ke jami'ar Copenhagen, ta ce ba ta yi wani mamaki ba kan yadda aka rabu tsakanin maza da mata wajen sanya takunkumi.
Ta bayyana yadda binciken da makarantu suka yi wadanda suka nuna yadda maza ke tunkarar abubuwa ta fuskoki daban-daban.
Kuma Gravert ta fada wa BBC yadda wani bincike mai sauki da aka gudanar da babban birnin Denmark ya nuna yadda mata suka fi mayar da hankali wajen kokarin shawo kan wannan annoba.

Asalin hoton, University of Oregon
Akwai banbance-banbancen jinsi a tsakanin kasashen yankin Asiya in da sanya takunkumi ya dade a matsayin wata al'adarsu.
Wani binciken bainar jama'a da aka yi a 2002-03 lokacin annobar Sars a Hong Kong ya nuna mata sun fi daukar matakan kariya kamar wanke hannu da sanya takunkumi.
Yayin murar 1918 da ta janyo mutuwar mutane sama da miliyan 10 a duniya, manyan maza da kananan jami'an lafiya suka nemi su bai wa shawara kan sanya takunkumi.
Abin farin ciki
Amma akwai kwararan shaidu kan cewa matsi daga abokan zama na taimakawa - kamar labarin Eduardo da Monica matarsa, wadanda suka rabu saboda takunkumi.
Bayan boren da Monica ta yi wa mijinta daga baya ta ga sauyi mai yawa. a karshe ta yi farin ciki: Eduardo ya koma sanya takunkumi yanzu.
"Yanzu na san miji na lafiyayye ne ina da tabbacin ba zan dauki cuta dagaa jikinsa ba," ta kara da cewa.
Mun sauya sunayen ma'auratan ne domin kiyaye kimarsu da sirrinsu.











