'Yan Shi'a sun yi nasara, an katse hanzarin Buhari: Abubuwan da suka faru a Najeriya makon nan

Asalin hoton, Getty Images
Mako ya kare ya bar mu da waiwaye kan manyan abubuwan da suka faru a cikinsa.
Ga dai wasu abubuwa da suka faru a makon da ya jiya daga ranar Litinin 29 ga watan Yuni zuwa Asabar 4 ga watan Yuli a Najeriya a takaice.
Sabbin matakan gwamnatin Najeriya na kullen cutar korona
A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta sake gabatar wa 'yan kasar sabbin matakai kan kullen annobar cutar korona.
Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar sun haɗa da ɗage haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi amma a lokutan da dokar takaita zirga-zirga ba ta aiki.
Domin karanta sauran matakan, sai ku latsa nan.

Yadda aka yi wa 'yar shekara 6 fyade aka jefar da gawarta a masallaci a Kaduna
A ranar Litinin din ne dai kuma hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya suka tabbatar da cewa yarinyar nan da aka ga gawarta a wani masallaci a wancan makon fyade ne aka yi mata.
Kwamishinar kula da harkokin mata da walwalar jama'a ta jihar ta shaida wa BBC cewa rahoton binciken da ta samu ya nuna cewa fyade aka yi mata kuma ta ce jami'an tsaro sun dukufa don gano wanda ya yi mata fyaden.
Domin karanta cikakken labarin, sai ku latsa nan.
Litinin ba ta kare ba sai da wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci 'yan sandan Najeriya su biya 'yan kungiyar Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzaky Naira miliyan 15 saboda kisan 'ya'yan kungiyar uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.

Aikin samar da bututun iskar gas a Najeriya
A ranar Talata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron kaddamar da katafaren aikin shimfida bututun isakar gas da zai hada kudanci da arewacin kasar mai nisan kilomita 614.
Aikin zai soma ne daga Ajaokuta ya bi ta Kaduna sannan ya wuce Kano. Ga dai abu bakwai da kuke bukatar sani kan aikin, wanda kamfanonin China biyu ne za su yi.
A wannan rana ce dai kuma rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu 'yan kasar China biyu bisa zargin kulle wasu 'yan Najeriya inda suka kwashe wata hudu suna tursasa musu yin aiki a otal dinsu.
Mutanen sun kwashe tsawon lokaci suna yin aikau a otal din na 'yan China da ke unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, amma ba a hana su shiga da fita ba sai watanni hudu da suka wuce lokacin da annobar korona ta yawaita a kasashen duniya.
ISWAP na son Najeriya ta biya ta fansa
Ita kuwa ranar Laraba ta zo ne da wata bukata ta mayakan kungiyar Boko Haram ɓangaren Albarnawi wato ISWAP, inda suka nemi a ba su dala dubu ɗari biyar kwatankwacin N190m kafin sakin wasu ma'aikatan agaji huɗu da wani jami'in tsaro da suka kama.
A ranar ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran ma'aikatan gwamnati da su guji amfani da matsayinsu wurin nemo aiki ga waɗanda suke so.
Larabar ba ta shude ba sai da gwamnatin Najeriya ta sanya ranar dawowar zirga-zirgar jiragen sama a cikin gida.

Asalin hoton, Hadi Sirika Twitter
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya bayyana hakan inda ya ce za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama daga Abuja babban birnin kasar zuwa Legas daga ranar Laraba 8 ga watan Yunin da muke ciki.
'Yan majalisa sun dakatar da shirin Buhari
A ranar Alhamis kuwa Majalisun Tarayya a Najeriya suka dakatar da shirin gwamnatin ƙasar na ɗaukar ma'aikata masu ƙaramin ƙarfi 774,000 har sai sun samu cikakken bayani kan tsarin ɗaukar mutanen da za su ci gajiyar shirin.
Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama'ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito.
Ssai ku latsa nan. don karanta sauran labarin.

Sabuwar kungiyar siyasa a Najeriya
A ranar Alhamis din ne dai wasu fitattun masu fafutukar kare hakkin bil'adama da wasu kwararru sun kafa wata sabuwar kungiyar siyasa a Najeriya.
Cikin wata sanarwar da ta rarraba wa manema labarai, kungiyar ta ce ba ta fito ba sai da ta shirya, kasancewar 'ya'yan kungiyar sun shafe wata guda suna tuntubar juna, kana suka ga lokacin fitowa a sarari ya yi.
Alhamis ba ta kare ba sai da aka samu labarin yadda Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta miƙa dan Najeriyar nan da ake zargi da damfara, Raymond Igbalode Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, ga hukumar bincike ta FBI a Amurka.
'Yan sandan Dubai ne suka sanar da hakan a wani sako da suka wallafa a shafinsu na Twitter.
Shugaban hukumar FBI Christopher Wray ya yabi 'yan sandan Dubai kan wannan gagarumin aiki na kama "Hushpuppi" da Olalekan Jacob Ponle da aka fi sani da "Woodberry" a samamen nasu na "Fox Hunt 2".
Kadan kenan daga cikin abubuwan da suka faru a makon nan. Kuna iya ziyartar shafinmu na bbc.hausa.com don duba sauran labarai da rahotanni kan Najeriya da sauran kasashen duniya.

Karin labaran da za ku so ku karanta













