Coronavirus a Najeriya: An sa ranar dawowar sufurin jiragen sama a kasar

@Hadisirika Twitter

Asalin hoton, @Hadisirika Twitter

Bayanan hoto, Za a sanar da ranar dawowar zirga-zirgar jiragen kasa da kasa idon hali ya bayar da damar hakan

Gwamnatin Najeriya ta sanya ranar dawowar zirga-zirgar jiragen sama a cikin gida.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na tuwita ranar Laraba.

Hadi Sirika ya ce za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama daga Abuja babban birnin kasar zuwa Legas daga ranar Laraba 8 ga watan Yunin da muke ciki.

Sanarwar ta kuma ce tashoshin jiragen sama na Kano da Fatakwal da Owerri da Maiduguri za su koma aiki daga ranar 11 ga watan na Yuni.

Sauran filayen jiragen sama kuma za a buɗe su don fara jigilar fasinja daga ranar 15 ga watan Yuni.

GETTY

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a sanar da ranar dawowar zirga-zirgar jiragen kasa da kasa idon hali ya bayar da damar hakan

Sai dai ya ce za a sanar da dawowa zirga-zirgar jiragen sama masu jigilar ƙasashe nan gaba idan hali ya ba da damar hakan.

A ranar Litinin ne kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar da sabbin matakan sassauta dokar kulle da aka ƙaƙaba a kasar.

Kwamitin ya sanar da bude tashoshin motoci da ci gaba da zirga-zirgarsu amma da ka'idoji kamar yadda aka bayyana.

Kazalika kwamitin shugaban ƙasar ya bayyana bude makarantu ga daliban da za su rubuta jarrabawar karshe a makarantu amma ya ce jami'o'i za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Zuwa yanzu dai cutar korona ta kama sama da mutum 25,000 a kasar kuma ta hallaka kimanin mutum 590.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Asalin hoton, NCDC